Zargin ɓatancin da ya haifar da cece-kuce tsakanin Tinubu da jam’iyyun PDP da LP

Assalam alaikum. Ina yi wa jaridar Bleuprint Manhaja fatan alkhairi.

Zargin ɓata suna da ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kan abokan hamayyarsa na PDP da LP na cigaba da haifar da ceku-cece tsakanin magoya bayan jam’iyyun.

Wannan batu ya fito fili ne lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya ce zai shigar da karar wasu kafofin yaɗa labarai da kuma jam’iyyun da ya zarga na yaɗa labaran karya domin vata masa suna da takararsa.

A ƙarshen makon jiya ne aka riƙa yawo da wata sanarwa da sunan hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, da ke cewa za ta binciki labaran da ke fitowa daga Amurka kan Bola Tinubu, da ke alaƙanta shi da harkar migayun ƙwayoyi.

Sai dai daga baya INEC ta fitar da sanarwa ta shafukanta na sada zumunta tana nesanta kanta da wannan sanarwa.

Lamarin ya harzuka jam’iyyar APC da tursasa mata fitar da sanarwa inda ta zargi PDP da LP da shirya mata manaƙisa.

Takardar da aka riƙa yawo da ita na cewa wata kotu a Amurka ta kwace wasu dalolin Amurka daga asusun Tinubu a yankin arewacin Illinois kan zargin alaqa da fataucin kwayoyi.

Sai dai kuma takardun ba su bada wasu bayanai ko tabbatar da cewa an yi wa Tinubu shari’a ba, ko kuma yana da alaƙa da wata ƙungiyar fataucin ƙwayoyi.

Takardun sun kuma nuna cewa anyi wannan shari’a ne shekaru 30 da suka gabata.

A cewar bayanan, wannan yanayi ne ya tursasa wa Tinubu sadaukar da kuɗaɗen da yawansu ya kai dala 460,000 a ɗaya daga cikin asusun bankunansa 10 da aka ce mallakar tsohon gwamnan Legas ɗin ne.

Sai dai kwamitin yaƙin neman zaven Tinubu ya ce an ba da wadannan kuɗaɗen ne a matsayin haraji da Tinubu ya jima bai bayar ba.

Sannan kwamitin ya zargi maƙiya da abokan hamayya irin su PDP da LP da amfani da wannan dama wajen shirya labaran ƙarya suna yaɗawa kan ɗan takarar shugabancin na APC.

Kwaimitin ya kuma yi barazanar ɗaukar matakan shari’a kan kafofin yaɗa labaran da suka yaɗa wannan labari ba tare da tantace sahihanci ko gaskiyar zance ba.

APC na son a yi bincike domin gano wanda ya soma yaɗa sanarwar ƙaryar da sunan INEC kan ɗan takararsu.

Sai dai babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta mayar da martani tana mai cewa tana da duk wata dama a doka ta ƙalubalantar takarar Bola Tinubu a APC, ciki har da cancantarsa a zaɓen 2023, la’akari da irin labaran da ake samu a kansa na saɓa doka da harkar migayun ƙwayoyi a Amurka.

A wani taron manema labarai, sakataren hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Debo Ologunagba, ya ce Bola Tinubu bai cancanci wannan takarar ba sakamakon zarge-zarge da ke fitowa a kansa.

PDP ta ce zura wa ɗan takarar ido a wannan tafiya barazana ce ga tsarin ƙasar na dimukuraɗiya da mutuncinta a idon duniya.

Sannan ta kuma zargi cewa irin barazanar da suka fuskanta a gangamin yaƙin neman zaɓensu a Kaduna da Borno na nuna ƙarara irin abin da APC za ta iya aikatawa.

Allah Ya sa mu dace.

Wasiƙa Daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.