Zargin amfani da takardun ƙarya: Kotu ta yi barazanar kulle Fani-Kayode

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kotun hukunta manyan laifuka da ke zamanta a Ikeja, Legas, ta ce, za ta bayyana tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo idan har ya kasa bayyana a rana mai zuwa da ta ɗage sauraron shari’arsa.

Mai shari’a Olubumni Abike-Fadipe ya koka kan rashin bayyanar da wanda ake tuhuma a kai a kai, inda ya bayyana cewa a karon ƙarshe da ya kai kotu shi ne ranar 4 ga watan Nuwamba, 2022.

Fani-Kayode dai yana fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 12 da suka haɗa da amfani da takardun ƙarya, yin amfani da hujjojin da aka ƙayyade, da laifin aiwatar da takardu ta hanyar ƙarya.

Ya amsa cewa “ba shi da laifi” a lokacin da aka fara gurfanar da shi a ranar 17 ga Disamba, 2021.

Bayan gurfanar da shi kuma aka fara shari’ar, wanda ake ƙara bai halarci shari’ar ba a aqalla kwanaki uku da aka ɗage ci gaba da sauraron ƙarar, lamarin da ya sa alƙali ya nuna takaicinsa.

A ranar da aka ɗage zaman na ƙarshe, lauyansa Wale Balogun, ya sanar da kotun rashin halartar wanda ake ƙara bisa dalilan rashin lafiya da kuma wasu batutuwa da aka ce yana da alaqa da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Balogun ya kuma roƙi kotun da ta ɗage shi tare da yin alƙawarin bayar da wanda yake karewa a zaman na ranar.

Da aka kira shari’ar a ranar, Chinozo Eze, wanda ya wakilci wanda ake ƙara ya shaida wa kotun cewa Fani-Kayode bai bayyana a gaban kotu ba ne saboda matsalar rashin lafiya.

Ya sanar da kotun cewa, rahoton likita da kuma wasiƙar neman izinin kotu na barin kwanaki biyun da aka jera domin sauraren ƙarar tuni yana cikin fayil ɗin kotun.

Lauyan Hukumar Yaqi da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), Zeenat Atiku ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta ce hannun masu gabatar da ƙara na ɗaure kan yadda za a yi a gaba.

Sai dai alƙali ya fusata kan yawan uzurin da wanda ake ƙara ke yi na rashin bayyanarsa.

Daga nan ne kotun ta ce, za ta bayar da sammaci kan Fani-Kayode idan ya gaza zuwa ranar da za ta saka a gaba.

Alƙalin ya kuma nuna rashin jin daɗinsa ga mai gabatar da ƙara kan rashin tuhumar da ake yi masa, inda ya ce, hukumar EFCC na iya janye batun idan ba ta shirya gurfanar da shi ba.

Mai shari’a Olubumni Abike-Fadipe ta ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 7 ga watan Nuwamba, 2023, domin ci gaba da shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *