Zargin badaƙalar kuɗi: Ya kamata hukumomi su yi bincike –Malagi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD HAMZA a Abuja

Alhaji Idris Mohammed Malagi, ɗaya daga cikin masu magana da yawun ɗan takarar jam’iyyar APC, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manema labarai a ciki har da Wakilin Blueprint Manhaja a ofishin kamfe ɗin Tinubu a Abuja dangane da tonon sililin da tsohon ma’aikacin Atiku Abubakar, ɗan takarar kujerar Shugaban Qasa na jam’iyyar PDP a 2023, Micheal Achimugu, ya yi na cewa, Atiku ya yi wasoson kuɗin jama’a lokacin da yake riƙe da muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Mene dalilin ganawa da manema labarai?

MALAGI: Abinda muke son sanar da Duniya shi ne, Jami’an tsaro su kama Alhaji Atiku Abubakar don akwai wasu kuɗi da aka yi sama da faɗi da su lokacin da yake mulki. Abinda muke cewa shi ne, hukumomin bincike su yi bincike a kan wannan al’amari don a tabbatar da gaskiyar wannan almundahana.

Wannan ana ganin ko siyasa ce mai zafi, maimakon a nemo mafita ga al’amuran da ke suka adabi Nijeriya?

Gaskiya hakan, amma ai an kai makwanni biyu da wannan tonon sililin ya fito, ba a yi magana ba sai yanzu. Muryar da hoton da aka fitar na wanda ake zargi da wannan takardu da aka fitar mako biyu kenan, amma abin yana ta yaɗuwa a kafafen yaɗa labarai, ba mu ce komai ba. Amma abin yana ta yaɗuwa a kafofin yaɗa labaru na sada zumunta, shi ya sa muka ce ya kamata a zo a sake ba da haske ga wannan al’amari saboda jami’an tsaro su yi nasu binciken. Kuma ba wannan abin ne kawai ake magana a kai ba kadai.

Shi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, maigidanmu ɗan takarar jam’iyyar APC yana da manufofin abinda yake so ya yi wa ƙasa Nijeriya.

Kwanakin baya da aka yi ta ce-ce-ku-cen cewa Tinubu yana hada-hadar ƙwayoyi a Amurka, mu ‘yan APC mun fito mun kare shi. Ya rage ne su kuma ‘yan PDP su fito su zo su kare shi. A matsayinmu na masu aikin fitowa mu yayata wannan almundahana, muna so jami’an tsaro da na bincike da sauran hukumomi su yi nasu aikin.

Me ku ke son ganin an yi?

Aikinmu mu faɗa, sannan aikin jami’an tsaro da sauransu, su bincika. Jam’iyyar APC ba ta hana a binciki ya’yan Jam’iyyar APC ba. Duk wanda ya yi laifi a APC ,ko a PDP ko Jam’iyyar Labour ko APGA, dole ne a bincike shi. Hukumomi ke da haƙƙin cewa wannan abin gaskiya ne, ko ba gaskiya ba ne.

Shin ko an binciki zargin Tinubu da harkar ƙwaya kafin a kawo nan?

Wasu ne suka yi wannan tonon sililin, mu masu kwarmatawa ne, wani ne ya fito da waɗannan shaidu, sannan haƙƙin Jami’an tsaro ne su yi bincike da tuhuma.

Idan aka yi binciken, kuma aka ce ba a ga laifi ba, shikenan, ko kuwa ya za a yi?

Jami’an tsaro dai ya dace su yi aikinsu. Abokin aikina da muke da alhakin yin magana da yawun Asiwaju Tinubu, Barrister Festus Keyamo ya ce ko da Tinubu da APC ba su yi komai ba, shi zai ɗauki gava ta kai ƙorafi. Ya ce in ba su yi bincike ba, shi zai yi. Ya kuma ce, ya riga ya rubuta takarda ga jami’an tsaro, cewa idan ba su yi bincike, shi zai yi. Mu dai mun yi aikin jaddada fallasasawa.

Za ka iya yi qarin bayani dalla-dalla a kan wannan badaqalar da ake ta yaɗawa?

Maganganu ne masu ɗan dama, ai ka gansu nan. Ababe ne ko shaidu da ake zargin ɗan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da yi. Takardun suna da yawa. Ana zargin an yi sama da faɗi da kuɗin Baitul Mali, shi wanda ya yi zargin yana da shaidu. ‘Yan mintoci ba zai ba mu damar yi bayani filla filla ba. Ana maganar cewa an yi sama da faɗi da kuɗin jama’a. Ya yi rantsuwa a kotu cewa shi tsohon ma’aikacin Atiku Abubakar ne, watau tsohon mataimakin shugaban ƙasa. 

Ku na son a binciki Atiku, amma a ƙyale Obasanjo, me ya sa ba ku ce komai kansa ba?

A’a, ba a ce a yi shiru ba. Abinda aka ce shi ne, duk wanda aka samu yana da hannu a wannan batun na almundahana, ya kamata a bincike shi. Ba wanda ya ce a yi shiru. Idan doka ta ce a bincike shi, a bincike shi kuma a hukunta shi. Doka ta san hukuncin da aka tanadar.

Kuna zargin cewa da wannan kuɗi aka kafa wannan jami’o’i guda biyu, na Atiku da na Obasanjo, kuna da hujja?

Mu ikonmu na ‘yan jarida shi ne, mu fito da abu a fili. Jami’an tsaro da na bincike su yi nasu binciken don a gano gaskiya da haƙiƙanin tabbacin wannan al’amari. 

Ba kwa tsoro wannan zai jefa ku cikin babban rikici?

Inda babu shaida ta haƙiƙa, da ba a isa a fito da wannan abun ba. 

Shin ko kuna da hujjojin cewa an yi wannan rub-da-cikin, da tabbacin cewa abinda kuka faɗa gaskiya ne?

Takardun da aka raba, akwai abubuwa da dama a ciki. Ka karanta ka gani. 

Ba ka ganin za a yi zargin wannan wata hanya ce da za ku yi amfani da ita don tallata ‘dan takararku ba?

Wasu ne suka fito da shi ba mu ba. Yadda ka gani, haka mu ma muka ɗauka muka yi amfani da shi. Muka ce ya kamata ku yi amfani da shi.  Tsohon Ma’aikacin Atiku ne ya yi wannan tonon sililin, shi fitar da muryar Atiku. Akwai abubuwa da yawa, mu mun je muna yin kamfe. Sati biyu kenan ana ta wannan aikin. Shi ya sa muke cewa ga abinda muke ciki. Muna jawo hankalin hukumomin tsaro don su bincika. 

Ku na nufin Atiku bai kamata ya yi takara ba kenan, watau ya janye daga takara saboda wannan badaƙalar da ake zargin ya tafka?

Ya kamata ya amsa kuma ya warware waɗannan badaƙalar tukunna.