Zargin da aka yi wa matsayin ƙasar Sin kan batun Ukraine maƙarƙashiya ce

Daga CRI HAUSA

Kafafen yaɗa labaran Amurka sun ruwaito cewa, matsayin ƙasar Sin kan batun ƙasar Ukraine, ya saɓa wa manufofin ta na yau da kullum, wato mutunta cikakken ‘yanci da yankin kowace ƙasa. Game da wannan zargin, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba cewa, zargin maƙarƙashiya ce da aka ƙulla, ko kuma yunƙuri ne na jirkita gaskiya.

Madam Hua ta yi nuni da cewa, ra’ayin ƙasar Sin kan batun Ukraine, ya yi daidai da matsayinta a kullum, wato daidaita matsaloli ta hanyar yin shawarwari. Ƙasar Sin tana tsayawa haiƙan, kan tabbatar da adalci da zaman lafiya, da yin kira ga ƙasa da ƙasa, su lalubo bakin zaren daidaita rikicin duniya bisa ƙa’dioji, gami da manufofin kundin tsarin mulkin MDD.

A wani labarin na daban kuma, Madam Hua ta zargi wasu ‘yan siyasar yankin Taiwan na ƙasar Sin, da kwatanta batun Ukraine da batun Taiwan, inda a cewarta, Taiwan ba Ukraine ba ce, kana, yin amfani da batun Ukraine don rura wutar rikici da wasu ‘yan siyasar Taiwan suke yi, rashin tunani ne.

Hua ta yi karin haske da cewa, batun Taiwan ya samo asali ne daga yaƙin basasar da aka yi wasu shekaru da suka wuce, al’amarin da ya janyo rikicin siyasa tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan. Amma ba’a taba ware Taiwan daga cikin ƙasar Sin ba, kuma hakan ba zai faru ba, wannan shi ne gaskiyar lamari.

Fassarawa: Murtala Zhang