Zargin maguɗi: INEC ta dakatar da Kwamishin Zaɓe na Sakkwato

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Sakkwato, Nura Ali, bisa zargin tafka maguɗi.

Bayanin dakatarwar na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai ɗauke da sa hannun Sakatariyar INEC, Rose Orlaran-Anthony, wadda hukumar ta aike wa Kwamishinan da kuma Sakataren hukumar na Jihar Sakkwato.

A cewar wasiƙar mai ɗauke da lamba: INEC/SCE/442/V.II, “Wannan shi ne don sanar da matsayar hukumar a kanka (Dr Nura Ali), Kwamishinan Zaɓe na Jihar Sakkwato, cewa ka yi nesa da ofishin hukumar a Jihar Sakkwato har sai abin da hali ya yi.”

INEC ta ba da umarnin Sakataren gudanarwa na hukumar a Sakkwato, Aliyu Kangiwa, ya maye gurbin Nura Ali wajen ci gaba da kula da hukumar.

Duk da dai wasiƙar ba ta bayyana cikakken dalilin da ya sa aka dakatar da Kwamishinan ba, sai dai Jaridar Daily Nigerian ta ce hakan ba ya rasa nasaba da zargin tafka maguɗi a zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu a jihar.