Zargin tauye haƙƙi: Kotu ta yi watsi da ƙarar Kanu kan SSS

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Babban Birnin Tarayya, a ranar Alhamis, ta yi watsi da ƙarar da Nnamdi Kanu, Shugaban haramtacciyar ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biyafar (IPOB), ya shigar a kan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS).

Mai shari’a James Omotosho, a cikin hukuncin da ya yanke, ya ce, ƙarar Kanu ba ta da inganci kuma ya kamata a yi watsi da ita.

Kanu, a ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/482/2022 da lauyansa ya shigar, ya maka Darakta Janar na DSS da Atoni-Janar na Tarayya, AGF, a matsayin masu amsa na 1 zuwa 3.

A cikin ƙarar, shugaban na IPOB ya yi zargin cewa DSS na cin zarafinsa a lokuta daban-daban, ciki har da hana shi haƙƙin sa na sanya duk wani kayan da ya ga dama kamar rigar gargajiyar qabilar Igbo da ake kira “Isi-Agu,” yayin da yake tsare a wurin su ko lokacin da ya bayyana a gaban kotu domin shari’ar sa.

Ya yi zargin cewa jami’an tsaron da ke hannunsu sun ba wa sauran fursunonin da ke hannunsu ’yancin zaɓar ko sanya duk wani tufafin da suka ga dama, amma an hana shi hakan.

Mai shigar da ƙarar ya kuma zargi hukumar SSS da azabtar da shi, tauye haƙƙinsa na mutunci da sauransu.

Don haka ya nemi a umurci waɗanda ake ƙara da su ba shi damar sanya duk wata rigar da ya ga dama yayin da yake cikin wurin ko kuma a lokacin da ya bayyana a bainar jama’a, da dai sauransu.

Sai dai a takardar ƙarar da hukumar SSS da shugabanta suka shigar, sun buƙaci kotun ta yi watsi da ikirarin Kanu.

Sun ce, jami’an nasu ba su taɓa azabtar da Kanu ba ko dai a jiki ko kuma a lokacin da suke tsare da shi ba.

A cewar hukumar ta SSS, su na ajiye Kanu ne a wurin su inda ake ajiye duk wasu da ake zargi.

Sun ce ba gaskiya ba ne a ce an bar sauran waɗanda ake zargin su sanya duk wani suturar da suka ga dama da suka haɗa da na Hausa da na Yarabawa.

Sun ce wurin ba wurin shaƙatawa ba ne ko bikin gargajiya inda za a bar Kanu da sauran waɗanda ake zargi su yi ado da kayansu na gargajiya.

Sun yi ikirarin cewa akwai ƙa’idar Aiki, SOP, kan ƙa’idojin tufafi na mutane a cikin wuraren su.

“Abin da ya yi daidai da kyawawan halaye na duniya, an ba wa mutanen da ke na 1 da na 2 damar sanya tufafin da ba su da alamomi, rubuce-rubuce, launuka da alamomi waɗanda ke cin zarafi ga kowane addini, ƙabila ko ma Nijeriya gaba ɗaya,” in ji su.

Sun zargi iyalan Kanu da kawo kayan gargajiya da wasu kayan sawa masu alamar Biyafara da jajayen takalmi da aka yi wa ado da gyale mai sheqi domin ya saka a gidan yari da kuma zuwa kotu domin gurfanar da shi.

A cewar SSS, tufafin suna da launuka na jamhuriyar Biyafara da ba ta wanzu ba, wanda shine batun shari’ar masu laifi.

Sun ce rigar Isi-Agu, wacce aka fi sani da rigar sarauta, ba ta dace da mutanen da ake tsare da su ba, kuma sun sava wa SOP.

Sun kuma yi zargin cewa Mai shari’a Binta Nyako, inda Kanu yake shari’a a halin yanzu, ta bayar da umarnin a bar Kanu ya saka duk wata rigar da yake so, kuma duk wani abu da ya sava wa umarnin kotu.

Hukumar SSS ta ce, ba su taɓa keta haƙƙinsa na mutunta ɗan Adam ba kamar yadda shugaban IPOB ɗin ya yi zargin.

Da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Omotosho ya ce, haƙƙin ɗan Adam yana ƙunshe ne a sashe na 34 na Kundin Tsarin Mulkin ƙasar na 1999.

Ya ce, a fili yake cewa haƙƙi na mutunta ɗan Adam da ya shafi haƙƙi na azabtarwa cin zarafi da sauransu.

Alqalin kotun ya ce, shari’ar Kanu ba ta da alaƙa da azabtarwa ko kuma aikin tilas domin ba a taɓa azabtar da shi ba yayin da yake tsare bisa ga hujjojin da ke gaban kotu.

Ya ce, haƙƙin mutuntaka ba haƙƙin canja kaya a matsayin fursuna a gidan yari ba ne.