Zazzaɓin Lasa ya kashe ‘yan Nijeriya 170, Ƙyandar Biri ta kashe mutum shida

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Cibiyar Yaƙi da Cutattuka ta Nijeriya (NCDC), ta bayyana cewar Zazzaɓin Lasa ya kashe ‘yan Nijeriya kimanin 170 a cikin jihohi guda 25 na ƙasar nan, tun daga farkon wannan shekara zuwa wannan lokaci.

Cibiyar, a cikin rahoton ta na loto-loto da ta fitar a ranar Juma’a da ta gabata, ta ƙara da cewar, an samu tabbatattun kamuwar cutar a jikin mutane 909, daga cikin mutane 6, 547 da aka yi hasashen kamuwarsu a tsakanin wannan lokaci.

Ta ce, “a jimlace, daga makon farko zuwa makonni 35 na shekarar 2022, an samu mace-macen mutane 170, wanda varnar kawo mutuwar (CFR) ta kai kashi 18.7 cikin ɗari wanda yake ƙasa da CFR na shekarar 2021 mai kashi 22.7 cikin ɗari na kwatankwacin wancan lokaci.

“A jimlace a shekarar 2022, jihohi ashirin da biyar a taƙaice an samu tabbacin kamuwar cutar na mutum guda a kowace jiha na qananan hukumomi 101 na waɗannan jihohi da aka jimlata.”

Rahoton cibiyar ya kuma bayyana cewar, a ɗaukacin mutanen da aka tabbatar suna ɗauke da cutar, kashi 70 cikin ɗari suna cikin waɗannan jihohi ne na Ondo 31%, Edo 26% da Bauchi 13%

Rahoton ya kuma bayyana cewar, waɗanda ake asshakar kamuwarsu ya ɗara sama da na daidai wannan lokaci na shekarar da ta gabata ta 2021.

Har wa yau, rahoton ya ce a sati na 35, daga 29 ga watan Agusta zuwa 4 ga watan Satumba da muke ciki, yawan waɗanda suka kamu da cutar, ya yawaita daga kamuwa biyar 5 a sati guda na 34 zuwa kamuwa goma a wannan sati mai shuɗewa.

“Waɗannan sun bayyana ne daga jihohin Ondo, Edo da Nasarawa,” kamar yadda rahoton ya zayyana.

Rahoton ya kuma bayyana cewar, babu wani ma’aikacin lafiya da ya kamu a wannan sati na talatin da biyar da muke ciki.

Dangane da rahoton cutar Ƙyandar Biri kuma, cibiyar ta bayyana cewar, an samu jimlar mutane talatin da shida da suka kamu da cutar a cikin jihohi goma sha huɗu a cikin sati ɗaya.

Rahoton ya bayyana cewar, an samu asshakar kamuwar mutane ɗari a sati na talatin da huɗu na shekarar, lokacin da cutar ta hauhawa (a tsakanin 22 zuwa 28 ga watan Agusta, 2022), waɗanda daga cikinsu aka tabbatar da kamuwar mutanen talatin da shida.

A cikin jihohi sha huɗu da aka tabbatar da kamuwar cutar, Legas tana da bakwai, Abia shida, Bayelsa biyar, Edo uku, Ondo uku, Delta biyu, Ebonyi biyu, Ribas biyu, Anambra ɗaya, Benuwai ɗaya, Gombe ɗaya, Imo ɗaya, Katsina ɗaya da Oyo ɗaya.

Rahoton ya kuma bayyana cewar, an tabbatar da mutuwar mutane shida da suka jiɓanci cutar Ƙyandar Biri a jihohi shida, inda kowace jiha take da mutum guda a kuma wannan shekara ta 2022 da suka haɗa da jihohin Delta, Legas, Ondo 1, Akwa Ibom 1, Kogi 1 da Taraba 1.

Ta ce, a dunƙule dai daga 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, Nijeriya ta lissafa mutane da ake asshakar su da kamuwa daga cutar Ƙyandar Biri guda 704, waɗanda daga cikinsu aka tabbatar da kamuwar mutune ɗari biyu da saba’in da bakwai (maza 186, mata 91) daga jihohi talatin na tarayyar Nijeriya.