Zeɓen sabon Shugaban APC

Ban yi mamaki da samun nasara ga Sanata Abdullahi Adamu, wanda ya fito daga jihar Nasarawa ba.

Tun farko kafin a je ranar zaɓen an tsammaci cewa za ai maslaha a madadin a yi zaɓe kuma hakan a kai. Tabbas hakan ke ƙara fitar da tagomashi da nagarta ga shugabancin jam’iyya mai mulki APC ganin duk waɗancen jiga-jigai sun janye tare da amincewa da mutum guda ya zamo shugaban jam’iyya na ƙasa.

A gefe guda ga kuma shugaban matasa na ƙasa Komrat Dayo wanda hakan ma wata nasara ce ga matasa da fatan duk waɗanda a ka zaɓa su zamo ma su kwatanta gaskiya da adalci kuma su zamo ma su haƙuri da sauraren al’umma. Allah ya yi maku jagora a mulkinku, amin.

Saƙo Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa. Katsina. 07066434519 – 08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *