Daga CMG HAUSA
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya musanta zargin da Amurka ta yi, cewa wai Sin na taimakawa ƙasar Rasha a fannin yaɗa bayanan bogi, yana mai cewa, irin waɗannan kalamai na Amurka, manyan ƙarairayi ne da ƙasar ke yaɗawa duniya, wanda hakan ya dada tabbatar da Amurka a matsayin wadda ta yi matuƙar ƙwarewa wajen kitsa kalaman bogi.
Zhao Lijian ya kuma ce Sin na kan bakan ta, na kin amincewa da matakin Amurka, na fakewa da batun kare haƙƙin bil adama, da amfani da ƙarfin gwamnati wajen yiwa kamfanonin Sin matsin lamba.
Ya ce duk da yanayi na rashin daidaito da tabbashi, har kullum tattalin arzikin Sin na ci gaba da zaburar da tattalin arzikin duniya.
Mai fassarawa: Saminu daga CMG Hausa