Zhao Lijian: Taron sassa 4 wani yunƙuri ne na daƙile ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce taron da manyan jami’an ƙasashen Amurka da Japan, da Australia da Indiya suka shirya gudanarwa, wani salo ne na yunƙurin daƙile ƙasar Sin.

Zhao wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana, ya ce sassan 4 na da burin amfani da taron na su, domin tattauna abun da suka kira “ƙaruwar tasirin Sin”.


Jami’in ya ƙara da cewa, wannan salo ne da Amurka ke bi domin wanzar da danniya, kuma hakan zai harzuƙa wasu sassa, tare da haifar da fito na fito, tare da gurgunta haɗin gwiwar sassan ƙasa da ƙasa.

Zhao Lijian ya yi kira ga ƙasashen duniya, da su yi watsi da tsohon tsarin cacar baka, su gyara kura-kuran su, game da kafa tawagogin da za su riƙa yi wa saura kallon hadarin kaji, ko raba kan ƙasashen duniya. Kaza lika ya buƙaci sassan ƙasa da ƙasa, da su bada gudummawa, wajen wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin Asiya da tekun fasifik.

A Juma’ar nan ne, sakataren wajen Amurka Antony Blinken, ya gana da ministocin harkokin wajen ƙasashen Japan, da Australia, da Indiya a birnin Melbourne.