Zhao Lijian: Ya kamata a binciki ayyukan sojin Amurka masu nasaba da gwaje-gwajen ƙwayoyin halittu

Dag CRI HAUSA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya ce kamata ya yi a binciki ayyukan sojin Amurka, masu nasaba da makamai masu guba a gida da waje, domin sassan ƙasa da ƙasa su tantance abubuwan da Amurkan ke aiwatarwa.

Zhao na wannan tsokaci ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa, game da cibiyar gwaje gwajen ƙwayoyin halittu ta Amurka dake ƙasar Ukraine.

Zhao Lijian, ya ce cibiyar gwaje gwajen mai nasaba da ayyukan soji ta Amurka dake Ukraine, ɗan ƙaramin ɓangare ne kawai na makamantan ta da Amurka ke gudanarwa.

Amurka na da manufar da ta kira “Ta ƙarfafa tsarin kiwon lafiya na duniya”, wanda a ƙarƙashin ta, ma’aikatar tsaron ƙasar ke ɗaukar nauyin ɗakunan gwaje gwaje na ƙwayoyin halittu har 336 a ƙasashe 30.

Fassarawa: Saminu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *