Daga CMG HAUSA
Batun kare haƙƙin dan Adam batu ne mai muhimmanci ga al’ummar duniya. Sai dai, wasu na fakewa da shi wajen yayata manufarsu da ingiza rikici da ta da zaune tsaye.
A jiya ne shugabar hukumar kare haƙƙin dan Adam ta MDD, Michelle Bachelet ta fara ziyara a ƙasar Sin, inda za ta ziyarci lardunan Guandong da kuma jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta.
Ƙasar Sin ta shafe shekaru da dama tana fuskantar suka daga ƙasashen yamma ta hanyar ruruta batun kare haƙƙin dan Adam a ƙasar, musammam ma a jihar Xinjiang.
Ƙasar Sin ta sha nanata cewa tana maraba da jami’ai daga waɗannan ƙasashe da ba su taba ganin yanayin jihar Xinjiang ba, su ziyarci jihar don ganewa idanunsu yadda al’umma suke rayuwa cikin yanayin na kwanciyar hankali da wadata.
Ziyarar Michelle Bachelet, na zaman shaidar cewa, da gaske ƙasar Sin take, kuma ba ta da abun ɓoye dangane da yanayin da al’ummarta ke ciki. Duk wanda ke bibiyar yanayin ƙasar Sin ko ya ziyarci ƙasar, ya san cewa, tana dagewa wajen tabbatar da kare al’ummarta. Kana ba ta taba musanta daukar mataki kan ’yan ta’adda a jihar Xinjiang ba, matakan da kawo yanzu suka haifar da da mai ido ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin al’ummar yankin. Kazalika, sun samu goyon baya daga ƙasashen musulmi da ma waɗanda suke fuskantar hare-haren ta’addanci.
Fatan a yanzu shi ne, wannan ziyara ta shugabar hukumar kare haƙƙin dan Adam, za ta ƙara fahimtar da al’ummar duniya manufar ƙasashen yamma kan Sin, kuma shugabar za ta fayyace ainihin abun da ta gani domin wanke Sin din daga zarge-zarge marasa tushe da ake mata.
Fassarawa: Faeza Mustapha