Ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan ta tsananta halin da yankin ke ciki tare da zubar da ƙimar Amurka a duniya

DAGA MINA CMG HAUSA

Kwanan baya, kakakin majalisar wakilan ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta kai ziyara yankin Taiwan na kasar Sin, matakin da ya saƙawa ƙa’idar “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya” da sanarwoyin haɗin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma. Yau “Duniya a zanen MINA”, na bayani ne kan burin da Pelosi ke neman cimmawa a wannan ziyararta.

Nancy Pelosi ta yi iƙirarin cewa, ba za ta manta da alƙawarin da ta yi game da yankin ba, matakin da ya baiwa ‘yan Aware na Taiwan damar neman taimako daga ƙasashen yamma, a yunƙurin neman ɓallewar yankin daga ƙasar Sin. Amma ainihin burinta shi ne fakewa da batun yankin Taiwan, don neman samun ƙuri’u a zaɓen tsakiyar wa’adi za a yi a ƙasar Amurka, tare da kawar da hankalin al’umma daga abubuwan kunya da iyalanta suka aikata, ta yadda za ta kiyaye kujerarta a majalisar, tare da samun karin moriya.

Ziyarar Pelosi a yankin Taiwan mai cike da burin siyasa, ba za ta kawowa yankin demokuraɗiyya ba, a maimakon haka, sai ma ya tsananta halin da ake ciki a yankin. ‘Yan siyasar Amurka irinta Pelosi waɗanda suka ci amanarsu don neman cimma burinsu na siyasa, sun zubar da kimarsu a duniya. Kuma daga kashe, za su girbi abin da suka shuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *