Ziyarar Nancy Pelosi zuwa Taiwan takala ce mai muguwar manufa

Daga LAWAL SALE

A daren Talatar 2 ga watan Agustan shekaran nan ne kakakin majalisar wakilan ƙasar Amurka Nancy Pelosi ta dira a tsibirin Taiwan na ƙasar Sin, duk da cewa ƙasar Sin ta gargaɗi ƙasar Amurka tun kafin Nancy Pelosi ta tashi daga Amurka.

Wannan halin dai irin na mai kunnen ƙashi da Amurka ta dauka na shirya ziyarar kakakin majalisa Pelosi dai abu ne wanda ya keta ‘yancin mulkin ƙasar Sin da tsokana da shiga sharo ba shanu a harkokin cikin gidan ƙasar.

Tun farko dai shuwagabanin ƙasashen biyu na Sin da Amurka wato Xi Jinping da Joe Biden sun tattauna a wayar tarho, inda shugaba Xi ya ja kunnen ƙasar ta Amurka da cewa duk wanda ya yi wasa da wuta to ya tabbatar da shi za ta kona.

Sanin kowa ne dai cewa ƙasar Sin ɗaya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na ƙasar, a kan wannan, ƙasar Amurka ma ba ta musanta haka ba domin Sin da Amurka sun cimma yarjejeniyar kulla hulɗar diplomasiyya a shekarar 1978, inda Amurkar ta amince da gwamnatin jamhuriyar jama’ar Sin a matsayin halastacciyar gwamnati ɗaya kacal na ƙasar ta Sin, kuma jama’ar Amurka za ta kiyaye hulɗa da jama’ar yankin Taiwan ta fannonin al’adu da ta kasuwanci da sauransu, amma ban da ta sassan gwamnati.

Taiwan dai tsibiri ne kuma yanki ne a ƙarƙashin jamhuriyar jama’ar Sin wanda yake kudu maso gabashin ƙasar.

Mutanen Taiwan dai Sinawa ne kuma yarensu da al’adunsu duka na Sinawa ne.

Haka kuma kamar yadda muka sani, Taiwan ba ƙasa mai zaman kanta ba ce kuma ba ta da mazauni a Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ko a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa irin na gwamnati, don haka ma ne, babban sakataren MƊD Antonio Guterres ya nuna rashin jin dadinsa da ziyarar Pelosi wadda take neman ta da zaune tsaye da kawo rudani a zaman lafiya a yankin gabashin Asiya da ma duniya baki ɗaya.

Babban sakatare Guterres ya yi bayani cewa za a tsaya tsayin daka kan ƙudurin kasancewar ƙasar Sin daya ce tak a duniya.

Ƙasashe dai fiye da 160 ma suka yi tir da ziyarar Pelosi da nuna goyon bayansu ga ƙasar Sin da kuma bayyana cewa ziyarar ta keta dokokin ƙasa da kasa da manufar nan ta ƙasar Sin daya ce tak a duniya kuma Taiwan yanki ne na ƙasar Sin.

Wannan ziyara dai a ganina na mai lura da harkokin ƙasashen waje, babban kuskure ne ƙasar Amurka ta tafka, kuma takala ce da yin katsalandan a harkokin cikin gida na ƙasar Sin.

Haka zalika, abin lura ne Amurka na yin amfani da gurbatacciyar siyasa a yankin Asiya domin wata manufarta.

A sakamakon sa ido da katutu da Amurka ke yi a yankin ya sa ƙasashe da dama suna yin tir da halayenta na neman fitina.

Hakazalika, ban da ta da zaune tsaye da tsokana da wata manufa ban ga amfanin da ziyarar Pelosi za ta kawo wa yankin Taiwan ba da kawo halin zaman doya da man ja a hulɗar da ke tsakanin kasar Sin da Amurka.

A yanzu haka dai wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin ƙasar Sin da Amurka a yayin da ƙasar Sin ta yi martani ta hanyar dakatar da wasu yarjejeniyoyi da ake yi tsakanin ƙasashen biyu a baya.

Ita ma Nancy Pelosi ta samu nata a yayin da ƙasar Sin ta kakaba mata tare da iyalanta takunkumai da suka dace da tanadin dokokin jamhuriyar jama’ar ƙasar Sin.

Wannan dai duk abubuwa ne waɗanda ya kamata ƙasar Amurka ta san cewa ƙasar Sin ba za ta zauna ta yi shiru ba idan aka ci zarafinta ba.

Ya kamata kuma Amurka ta lura cewa Allah wadai da ƙasashe suka yi a kan wannan ziyara wani abu ne da zai rage mata girmamawa a idon duniya baki ɗaya saboda abin da zai haifar sakamakon ziyarar zai iya shafar ƙasashen duniya da ba su san hawa ba bare sauka ba.