Zuciyata tana kallon baban mawaƙi Davido ne – Jaruma

Daga AISHA ASAS

Shaharariyyar ’yar nishaɗantarwa kuma ’yar kasuwa a kafafen sada zumunta, wacce duniya ta sani da Jaruma, ta bayyana kwaɗaituwarta da yin soyayya da mahaifin mawaƙi Davido, shahararren ɗan kasuwa Adedeji Adeleke.

Jaruma ta bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ta wallafa a shafinta na TikTok.

A cewar Jaruma, wadda ta yi suna a siyar da kayan mata, kuma ta ke fuskatantar zagi sakamakon yadda take tallan kayan nata, da ke ɗauke da batsa, ta bayyana cewa, kayan da ta jera a teburin da ke gabanta a yayin ɗaukar bidiyon, waɗanda kayan mata ne, ta ce, tanadi ne ta yi na musamman domin mahaifin mawaƙin, Adeleke, inda ta bayyana shi ne zuciyarta ke kallo, domin shi ne ya kasance “target” ɗin ta na gaba.