Zul-Hajj: An hori al’umma su dage da aikata alheri

Daga MUAZU HARDAWA a Madina

Yayin da aka shiga watan Zul-Hijja, wata na ƙarshe a kalanadar Musulunci, an hori al’umma musamman Musulmi, da su kara himma wajen aikata ibada da sauran ayyukan alheri.

Limamin masallacin Manzon Allah (S.A.W) da ke birnin Madina a ƙasar Saudiyya, shi ne ya yi wannan horo sa’inlin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma’a a ranar Juma’ar da ta gabata.

Huɗubar mai tsawon minti 30, ta maida hankali ne kan muhimmancin aikin Hajji da Umrah da kuma yin jihadi don daukaka kalmar Allah.

Limamin ya ce, dukkan nasara na daga wajen Ubangiji, don haka ya buƙaci jama’a su tsarkake zukatan su, su aikata ayyuka nagari haɗe da yawan ambaton Allah.

Haka nan, ya yi kira ga jama’a da a kyautata wa juna, a nisanci tada fitina a tsakani, a bi umarnin Allah zuwa masallatanSa masu tsarki don bauta da yin sallah da ambaton Allah wanda ke arzuta bayainsa yadda Ya so.

Kazaliak, huɗubar ta buƙaci mutane su riƙa kiyaye harsunansu wajen faɗin gaskiya da nisantar cutar da juna, a kyautata wa musakai da masu ƙaramin ƙarfi, a bi maganar Allah da kiyaye dokokinSa.

Har wa yau, huɗubar ta ja hankalin mahajjata a kan su guji aikata fasikanci, ko jidali, ko tashin hankali kamar yadda ya zo cikin Alƙur’ani maigirma kuma Manzo (SAW) ya yi umarni a cikin Hadisansa.

Huɗuba ta biyu kuwa, ta fara ne da gode wa Allah da salati ga Manzo (SAW), daga nan ta buƙaci mutane su gode wa Allah, su bi umarni Manzo (SAW) wajen bauta wa Allah Maɗaukakin Sarki.

Huɗubar ta ci gaba da magana kan muhimmancin aikin Hajji da yin sallah cikin jam’i da nasihohi masu yawa don mutane su dace da rahamar Allah (SWT).

Bugu da ƙari, limamin ya jaddada muhimmancin azumin ranar Arfa da tsayuwar ranar Arfa, inda a ƙarshe ya yi addu’o’i tare da roƙon Allah Ya karɓi ayyukan mahajjata da kuma nema wa bayin Allah gafara.