Daga BASHIR ISAH
A matsayin ɓangare na ƙoƙarin da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ke yi don rage wa talakawansa raɗaɗin cire tallafin mai, Gwamnan ya saki manyan motocin bas-bas guda 80 haɗi da na ɗaukar kaya domin jigilar manona zuwa gona kyauta.
A ranar Talata Zulum ya saki motocin don fara aiki kamar yadda aka tsara.
Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan da mayaƙan Boko Haram suka kai hare-hare a yankin Wulari inda suka kashe manoma takwas, da kuma yankin Bulajimban tare yi wa manoma bakwai yankan rago.
Yayin da yake duba lafiyar hanyar da manoman za su yi amfani da ita, Gwamna Zulum ya samu tattaunawa da sojoji kan yadda za a samu a riƙa jigilar manoman cikin nasara.
A cewar Gwamnan, “Ana iya ganin dubban manoma a nan da ya wansu ya haura 10,000, muna ganin irin gudunmawar da sojoji da ‘yan sanda da dangoginsu ke bayarwa, sai dai wajibi ne mu waiwayi irin wahalar da waɗannan mutane ke fuskanta.”
Daga nan, ya yi kira ga jami’an tsaron da su ƙyale manoma su riƙa tafiya gona, saboda a cewarsa matsalar ƙarancin abinci ta fi tsanani bisa ga ta tsaro.