Zulum ya bada umarnin binciken ma’aikatan asibitin da suka ƙi karɓar waɗanda suka yi haɗari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya umurci ma’aikatar lafiya da ta yi bincike tare da kamo ma’aikatan lafiya da ke bakin aiki bisa zargin ƙin amincewa da waɗanda hatsari ya rutsa da su a asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da ke Maiduguri.

Zulum ya bayar da umarnin ne a ranar Alhamis a sashin bada agajin gaggawa na asibitin.
Ziyarar da gwamnan ya kai asibitin Umaru Shehu na zuwa ne a matsayin martani ga wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta wanda ke nuna yadda wasu jami’an kiwon lafiya suka ƙi amincewa da waɗanda hatsarin ya rutsa da su da aka kawo asibitin a rana da lokaci wanda masu bincike za su tantance.

Ya bada sa’o’i 24 ga ƙungiyar bincike don gano ma’aikatan kiwon lafiya da abin ya shafa da kuma bada shawarwarin da suka dace.

Abin da ya faru “rashin mutunci ne kuma ba abin yarda ba” Zulum ya ce yayin da yake jawabi ga ma’aikatan lafiya a asibitin.

“Yanayin da aka bar marasa lafiya suna kuka don neman taimako, amma asibiti ta ƙi karɓarsu?

“Ba za mu bar irin wannan abu yana farauwa ba. Ban ga dalilin da zai sa ba za a ɗauki matakin ladabtarwa a kan ma’aikatan da suka yi kuskure a wannan asibitin ba,” inji gwamnan.

“Idan duk wani likita ko wani ma’aikaci a kowane ɗayan wurarenmu ba ya son zuwa wurin marasa lafiya ba tare da wani dalili ba, to ya kamata a kore shi ko ita ba tare da vata lokaci ba,” inji Zulum.

Ya ƙara da cewa, “A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, ya kamata hukumar kula da asibitoci da ma’aikatar lafiya ta binciki lamarin tare da tabbatar da ɗaukar matakan ladabtarwa ga duk waɗanda ke bakin aiki da suka ki karvar waxanda haxarin ya rutsa da su.”

Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba jari sosai a fannin kiwon lafiya, ciki har da jin daɗin jami’an kiwon lafiya a faɗin jihar, don haka ya yi kira ga jami’an kiwon lafiya da su mayar da hankali wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga duk majinyata ba tare da nuna bambanci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *