Zulum ya amshi umarnin Buhari na dawo da aikin gona a yankin Mulai-Dalwa

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kai ziyara a ƙauyukan Mulai da Dalwa tare da ganawa da jami’an tsaro don samar da matakan da suka dace wajen farfaɗo da harkar noma a ƙauyukan.

A Lahadin da ta gabata Zulum ya yi wannan ziyarar a matsayin wani mataki na cika umarnin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda ya bayar sa’ilin da ya ziyarci jihar Alhamis da ta gabata, inda ya buƙaci jami’an tsaro su yi aiki tare da gwamnatin jihar wajen samar da tsare-tsaren da za su bai wa jama’ar ƙauyukan damar komawa gona ba tare da wata fargaba ko tsoro ba.

Yayin ziyarar aiki ta yini guda a jihar Borno, Buhari ya ce, “Na bai wa Kwamandan shirin Operation Hadin Kai da sauran hukumomin tsaro umarnin su yi aiki tare da Gwamnatin Borno da ƙungiyoyin manoma kan yadda za a faɗaɗa damar farfaɗo da ayyukan gona da kamun kifi da sauransu.”

Bisa wannan dalili ne Zulum ya ziyarci Dalwa da ke Konduga, da kuma Ngwom da ke yankin ƙaramar hukumar Mafa, inda ya gana da jami’an tsaron yankunan da kuma duba filayen noma da ake da su da zimmar farfaɗo da ayyukan noma.

Kafin wanna lokaci, Gwamna Zulum na ra’ayin cewa hana jama’a ci gaba da noma kamar yadda aka saba a can baya, hakan ka iya haifar da matsalar ƙarancin abinci a jihar. Yana mai cewa, tallafin abincin da ake samu daga cikin gida da ƙetare ba ya isa.

A cewar Zulum, “Dole mu lalubo mafita, ba zai yiwu mu zauna haka nan babu hanyar samar da aninci ba. Ni ma zan buɗe tawa gonar a yankin wanda zan riƙa zuwa a ranarkun da babu aiki.”