Zulum ya naɗa Indimi da wasu matsayin majalisar gudanarwa ta jami’ar Barno

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnan jihar Barno, Babagana Umara Zulum, ya naɗa Majalisar Gudanarwa da za ta sanya ido kan gudanar da harkokin Jami’ar Jihar Barno.

Zulum ya naɗa majalisar ne a ranar Litinin a fadar gwamnatin jihar, wadda za ta gudana ƙarƙashin jagorancin Alhaji Mohammed Indimi.

Sauran mambobin majalisar sun haɗa da Farfesa Abubakar Mustapha, Farfesa Bankole Ogumbameru, Farfesa Shettima Umara Bulakarima, Alhaji Lawan Buba, wakilin majalisar dattawa na jami’ar da dai sauransu, yayin da rajistaran jami’ar zai kasance riƙe da muƙamin sakataren majalisar.

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan majalisar da su samar da tsari mai inganci wajen gudanar da harkokinsu, tare da yin amfani da gwargwadon kayan aikin da jami’ar ke da shi wajen ciyar da ita gaba a dukkanin fannoni.

Kazalika, ya buƙace su da su assasa kyakkyawar dangantaka tsakanin jami’ar da takwarorinta domin bunƙasa sha’nin koyo da koyarwa a jami’ar.

Zulum ya bai wa majalisar tabbacin mara mata baya da kuma bada cikakken haɗin kan da jami’ar ke buƙata don kaiwa ga gaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *