Gwamna Uzodinma ya sauke kwamishinoni 20

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya sauke kwamishinoninsa 20 sannan ya rushe majalisar zartarwa ta jihar.

An bada sanarwar hakan ne jim kaɗan bayan kammala taron majalisar a Laraba a Owerri, babban birnin jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Declan Emelumba, ya shaida wa manema labarai cewa dalilin rushe majalisar shi ne, don sake wa gwamtin jihar tsare-tsaren gudanar da ayyukanta yadda ya kamata bayan da Gwamna Uzodinma ya cika shekara ɗaya da soma mulkin jihar.

Ya ƙara da cewa, daga cikin kwamishinoni 28 da jihar ke da su guda 8 ne kawai suka tsira.

Waɗanda suka tsira su ne; Kwamishinan Lafiya da na Yaɗa Labarai da na Yawon Shaƙatawa da ta Harkokin Mata da na Matasa, sai kuma na Ma’aikatar Fasaha.