Ƙalubalantar shawararar ziri ɗaya da hanya ɗaya? ‘Yan siyasar Amurka suna son tashi hannu rabbana

Daga CMG HAUSA

Amurka, wadda ba ta wadatu da ababen more rayuwa a cikin gidan ta ba , wai ita ce a zahiri za ta jagoranci aiwatar da abin da ake kira ayyukan samar da ababen more rayuwa a duniya. Wannan abin mamaki na rashin Imani,ya faru ne a taron G7 dake gudana a ƙasar Jamus.

A ranar 26 ga wata agogon wurin,a yayin taron, shugaban ƙasar Amurka Biden ya sanar da wani shiri na “haɗin gwiwar samar da abubuwan more rayuwa na ƙasa da ƙasa ” (PGII) inda ya yi iƙirarin yin aiki tare da ƙasashen G7, don tattara dalar Amurka biliyan 600, don zubawa a jarin samar da ababen more rayuwa a duniya nan da shekarar 2027.

A yayin taron G7 da aka gudanar shekara guda da suka gabata, an gabatar da shawarar haɗin gwiwa da ake kira “Sake gina duniya mai Kyau” (B3W), tare da shirin zuba jarin sama da dalar Amurka tiriliyan 40 kan buƙatun kayayyakin more rayuwa a kasashe masu tasowa. A wancan lokacin, Biden ya ce shirin zai fi dacewa da bukatun samar da ababen more rayuwa na ƙasashe daban-daban fiye da shirin ziri daya da hanya ɗaya da ƙasar Sin ta gabatar.

Amma an kusa soke Shirin, saboda nuna ɓangaranci a Amurka. Ya zuwa yanzu, adadin kuɗaɗen da aka saka a cikin ayyukan da ke da alaka, dalar Amurka miliyan 6 ne kawai, wannan shi ake kira “surutu ba tare da gani a ƙasa ba”.

A halin yanzu, ƙasashe masu tasowa suna fuskantar babban gibin kuɗaɗe wajen gina ababen more rayuwa. Haƙiƙa abu ne mai kyau, idan har da gaske ‘yan siyasar Amurka suna son ba da taimakon kuɗi. Amma idan har ba sa son bai wa ƙasashe masu tasowa gudummawa, amma suna son yin wasa da hankali ne, to ko da sabbin sharuɗɗan da suka ƙirƙira don tattara su, ba za su iya yaudarar wasu ba, kuma tun ba a je ko’ina ba,ba za su taba yin nasara ba.

Fassarawar Ibrahim