28
Sep
Jama'a sun shiga halin ruɗani game da shari'ar zaɓen gwamna a jihar Kaduna. Hakan ya faru ne bayan da wani rahoto ya nuna Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe na Gwamnan Jihar ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba. Bayan kimanin awa guda da fitan rahoton, sai aka sake ganin wani rahoto na daban na cewa, kotun ta tabbatar da nasarar da Gwamna Uba Sani ya samu a zaɓen wanda hakan ke nuni da shi ne zaɓaɓɓen gwamnan jihar. Da yake yi wa Jaridar News Point Nigeria ƙarin haske game da hukuncin ta waya, lauyan Gwamna Sani, Ibrahim H O…