Garin Alawa a Neja ya kama hanyar zama kufai saboda rashin tsaro

Daga BASHIR ISAH

Al’ummar garin Alawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja, na ci gaba da ficewa daga garin saboda tsoron barazanar ‘yan bindiga.

Wannan na faruwa ne sakamakon janye jami’an tsaro da aka yi daga yankin alhalin yankin na daga wuraren da ke fuskantar barazanar ‘yan ta’adda a jihar.

Ya zuwa yanzu gwamnatin jihar ba ta ce komai kan batun ba.

Majiyarmu ta ce muddin hukumomi ba su yi wani abu kan batun ba, yankin Alawa zai za zama kufai nan ba da daɗewa ba.