Iyalan malamar Islamiyar da aka halaka a Kaduna sun bayyana yadda suka yi bankwana da ita

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan Malama Ummulkhairi, wadda malamar Islamiya ce da aka halaka tare da ƙone gawarta bisa zargin ƙarya da aka ɗora mata da ya danganci satar yara a yankin Maraban Jos da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna sun faɗi yadda ganawarsu ta ƙarshe ta kasance.

Wasu mazauna yankin ne suka zargi Ummulkhairi, wadda mahaifiyar ‘ya’ya huɗu ce, da yunƙurin satar yara a lokacin da take kan hanyar zuwa Islamiyar yamma a ranar Lahadi.

Zargin ya yaɗu cikin hanzari, wanda a sanadiyyar haka ne mutane da dama suka farmake ta kana ‘yan sanda suka shiga tsakani tare da garzayawa da ita zuwa ofishinsu da ke kusa.

Amma daga bisani wasu ɗaruruwan fusatattun matasa sun yi cincirindo a bakin ofishin tare da shan ƙarfin jami’an da ke bakin aiki a yayin da suka nemi a bayar da ita domin su mata hukunci, lamarin da ya sa suka banka mata wuta bayan fitar da ita daga cikin ofishin.

Mijin marigayiyar mai suna Aliyu Mohammed ya ce ya shiga mawuyacin hali a lokacin da ya samu labarin rasuwar iyalin nasa, wanda aka sanar da shi a lokacin da yake wajen aikinsa.

Ya ce, an kira shi an sanar da shi cewa an kama matarsa tana yunƙurin satar yara, inda ya kira wani abokinsa ya tura shi wajen kafin shi ɗin ya karasa. A cewarsa, ko da ya je wajen har an ƙone gawarta.

Ya bayyana cewa, ta bar gida cikin aminci sun yi sallama ta ce masa ta fi makaranta, shi kuma ya ce mata “A dawo lafiya.”

Haka kuma, an ruwaito cewa surikar marigayiyar, Zainab Aliyu, wadda ta ce tana tare da Ummulkhairi a lokacin da abin ya faru, ta yi zargin cewa DPO’n ne ya fito da marigayiyar waje duk da gargaɗin da ta yi masa a lokacin al’amarin ya yi ƙamari.

Tuni dai ƙungiyar Amnesty International ta yi tir da faruwar al’amarin tare da kira da a gudanar da bincike mai zurfi a kai da kuma gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu a laifin, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Facebook.

Haka kuma ta yi kira da a binciki zargin cewa ‘yan sandan ne suka miƙa Ummulkhairi ga ɓata-garin da suka yi aika-aikan.

A wani ɓangare, rundunar ‘yan sanda a Kaduna, ta ce ta kama sama da mutane 80 da ake zargi da hannu a aikata ɗanyen aikin, inda kakakinta DSP Mansir Hassan ya ce ana cigaba da farautar sauran mutanen da ake zargi.

By Babaji