Isra’ila ta ƙi amince wa matakan Trump 15 na janye sojojinta a Gaza

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi watsi da shirin saɗurra 15 ga Gaza da Shugaba Donald Trump na Amurka ya goya wa baya a matsayin sharuɗɗan zaman lafiya, yana mai cewa sojojin Isra’ila ba za su janye daga yankin Falasɗinun ba har zai Hamas ta tabbatar da ajiye makamanta.

Netanyahu ya sanar da wannan matsaya ne a ranar Lahadi, yayin zama da manyan jami’an gwamnatinsa a wani yanayi da ka iya haifar da tsaiko ga yunƙurin zaman lafiya da ake shirin samarwa a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Netanyahu ya ce wajibi ne Hamas ta miƙa manya da ƙananan makamanta gaba ɗaya gabanin sojojin Isra’ila su fice daga Gaza.

Shirin, wanda Shugaba Trump ya gabatar, ya tanadi janyewar sojojin Isra’ila a matakai tare da aiwatar da kwance ɗamarar yaƙin Hamas.

A ɗaya ɓangaren, Hamas ta ce za ta yi la’akari da ajiye makamanta ne bayan Isra’ila ta janye gaba ɗaya daga Gaza da kuma kawo ƙarshen yaƙin. Sannan, ta danganta miƙa manyan makaman nata da sharuɗɗan da suka haɗa da kafa ƙasar Falasɗinu.

A nasa kalaman firaministan ya ƙi amince wa wannan ra’ayi, inda ya ce ba za a kafa ƙasar Falasɗinu ba matuƙar ke jagorancin Isra’ila.

Wannan saɓani ka iya haddasa rashin jituwa tsakanin Isra’ila da Amurka kan yadda za a aiwatar da shirin sulhun.

Hakan na zuwa ne yayin da Isra’ila ke shirin gudanar da zaɓe a watan Oktoba, inda ake sa ran batutuwan yaƙin Gaza da Iran za su kasance cikin manyan abubuwan da masu kaɗa ƙuri’a za su yi la’akari da su.

By Babaji

Leave a Reply