Gwamnatin Tarayya ta kwaso ‘yan Nijeriya 105 daga Afirka ta Kudu yayin sabbin hare-haren ƙyamar baƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ce ta sake ɗebo wasu ‘yan Nijeriya guda 105 daga ƙasar Afirka ta Kudu bayan aukuwar wasu sababbin hare-haren ƙyamar baƙi akan ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashen Afirka. Wannan tattara ta sa jimillar waɗanda Nijeriya ta kwaso daga ƙasar ta kai 1,821 tun bayan fara aikin a watan Yuni.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutanen da aka dawo da su gida Nijeriya sun haɗa da manya 82 da yara 23, waɗanda suka sauka a filin jiragen sama na Legas ta jirgin South African Airways Flight SA060 da misalin ƙarfe 8:30 na maraicen ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026, inda jami’an hukumomin gwamnati suka tarbe su.

Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje Oluwafemi Adeniyi ya fitar a ranar Asabar. A cewar ma’aikatar, wannan shi ne karo na 13 da ake kwaso ‘yan ƙasa daga Afirka ta Kudu tun bayan fara atisayen a ranar 10 ga Yuni, 2026, lamarin da ya kai jimillar mutanen da aka kwaso zuwa 1,821, wanda daga ciki gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin 1,388.

Ta bayyana cewa, tallafin da cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ya bayar na Dala 265,854 shi ne aka yi amfani da shi wajen ɗaukar nauyin mutum 100 daga cikin 105 ɗin domin kwaso mutane 500 daga Afirka ta Kudu ta hanyar tikiti ɗaya-ɗaya. Sauran biyar ɗin kuma sun samu ɗaukar nauyi ne daga wani ɗan Nijeriya mai zaman kansa.

Gwamnatin ta kuma yaba wa RCCG a ƙarƙashin jagorancin Fasto Enoch Adejare Adebayo bisa gudunmawar tallafinsa ga shirin kwaso ‘ya’yan Nijeriyar. Haka kuma, ta yi godiya ga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da suka haɗa hannu da ita wajen taimaka wa aikin dawo da ‘yan Nijeriya gida daga ƙasar kudancin Afirkan.

Kazalika, ma’aikatar ta ce gwamnatin tarayyar tana cigaba da nuna damuwarta akan hare-haren da ake ƙaddamarwa akan ‘yan Nijeriya da ‘ya’yan wasu ƙasashen Afirka da ke ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply