‘Yan sanda a Kano sun cafke ɓarawon wayoyin hannu, sun ƙwato 222 da wasu ababe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano, ta ce ta kama wani da ake zargin ƙasrugumin ɓarawo ne da ya fasa shaguna huɗu a City Centre Plaza da ke kasuwar waya ta Farm Centre a Kano, inda ta ƙwato kayayyakin da ya sace.

A wata sanarwa da Kakakinta, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Laraba, ya ce al’amarin ya auku ne da misalin ƙarfe 04:00 na asubahin ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026, inda aka gano cewa an fasa shaguna huɗu da ake siyar da kayan waya a cikinsu. A cewarsa, wani mai suna Mohammed Rabo, wanda shi ne Shugaban Tsaron flazar ne ya sanar da rundunar labarin aukuwar lamarin.

Akan haka ne rundunar ta aike da jami’an tsaro zuwa yankin domin gudanar da bincike a kai. A yayin da suka isa, sun riski wani mai suna Abba Abubakar mai shekaru 27, wanda ɗan yankin Brigade Quarters ne yana shawagi acikin flazar ɗauke da wani zarto da makuncin noti. A nan take aka kama shi tare da garzayawa da shi zuwa ofishin ‘yan sanda.

A lokacin da ake binciken sa, matashin ya amsa cewa shi ne wanda ya fasa shaguna huɗun kuma ya tsere da ababe kamar haka: kwamfutar laptop guda, wayar Samsung Tablet guda, ƙananan wayoyi 95, manyan wayoyi 127, ansakuwa guda, babban ƙundun caji, fuskar manyan wayoyi 17, na’urar gudanar da solar guda, baturin ajiyar caji 29, tsabar kuɗi na N350,000 da dai sauransu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka yi wajen kama mai laifin da ƙwato ababe masu darajar, yana mai tabbatar wa al’umma cewa za su cigaba da ƙoƙarin bai wa dukiyoyi da rayukansu kariya. Sannan, rundunar ta ce za a maka matashin a kotu da zarar an kammala bincike akansa domin ya fuskanci hukuncin doka.

By Babaji

Leave a Reply