Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A yayin da nake wannan rubutu, wasu malamai da limamai, da suka fito daga ƙungiyoyin addinai daban-daban, na Musulunci da Kirista suna halartar wani taron wayar da kai game da haɗarin yaɗa labaran ƙarya da jita-jita a cikin al’umma, ƙarƙashin cibiyar yaƙi da yaɗa labaran ƙarya ta Alƙalanci.
Manufar masu shirya taron shi ne a wayar da kan masu faɗa a ji a cikin al’umma kamar malaman addini, waɗanda kalaman su suke tasiri sosai a wajen al’umma, domin su fahimci yadda za su kaucewa amfani da kalmomin ko labaran da ba a tabbatar da ingancin su ba, a cikin wa’azozin su da karantarwar su.
Jihar Filato ta kasance jiha ta farko da aka fara wannan horarwa a ƙarƙashin wannan zango, bisa la’akari da irin yanayin da jihar ke ciki, inda bambancin addini da ƙabilanci yake tasiri sosai a zamantakewar al’ummar jihar, wanda kuma a dalilin haka zaman lafiya da fahimtar juna ya yi ƙaranci a jihar. Ba baƙon abu ba ne a jihar a wayi gari ana yaɗa wani labari marar tushe a bakunan jama’a ko ta wayoyin sadarwa, ana amfani da su don cimma wani buri na siyasa, ƙabilanci, ko na addini. Daga cikin irin waɗannan labarai na ƙarya da ake yaɗawa za ka ji ana cewa wasu mutane ’yan addini kaza, ko mabiya ƙungiyar addini kaza suna shirin kai wa wasu mutane hari. Ko kuma ka ji cewa wasu sun yi taro a waje kaza za su yi wani mugun abu kan wasu masu addini ko ƙabila kaza. Amma da zarar an bincika sai ka ga an tarar babu wamshin gaskiya cikin labarin.
Malaman addini a irin wannan yanayi su ne suke fuskantar ƙalubale mai yawa, saboda sau da dama irin waɗannan maganganu kan yi tasiri a cikin koyarwar da suke yi ko wa’azin da suke gabatarwa, da nufin jawo hankali kan abubuwan da suke zargi ana ƙullawa a ɓoye akan mutanen su. A wasu lokuta kuma mabiya kan yi amfani da tasirin malaman su wajen ba su labaran ƙarya da ba su inganta ba, don malaman su yi amfani da muryoyinsu wajen wara ruruta wutar da jita-jitar ta kunna.
Shi ya sa yake da kyau lokaci zuwa lokaci a riƙa shiryawa, malamai da masu wa’azi na addini, irin wannan bita, domin su fahimci yadda za su kuɓuta daga tarkon marasa son zaman lafiya. Ina iya tunawa wata shekara wani malamin addinin Musulunci ya yi wani wa’azi game da haɗarin barin matar aure aikin asibiti, wanda zai buƙaci ta je aikin kwana. A jawabin malamin ya yi zargin cewa akasarin mata masu zuwa aikin dare suna zuwa shashancin su ne kawai da abokan aiki maza ko wasu maza na daban, a yayin da mazajensu na aure ke gida suna tunanin sun je aiki ne.
Wannan zargi mai ƙarfi ya tayar da ƙura sosai a lokacin, musamman a kafafen sada zumunta, inda mutane suka yi ta bayyana mabambantan ra’ayoyi akan batun, har ma ya nemi kashe auren wasu mata ma’aikatan jinya da dama. A ƙarshen al’amarin sai da ƙungiyar ma’aikatan jinya ta nemi ganawa da malamin domin warware batun, inda shi kuma ya bayyana cewa, wasu almajiran sa ne suka gaya masa abubuwan da ke faruwa. Shi kuma saboda amincewar da ya yi musu ya yarda da labarin har ya yi amfani da mumbarin sa na wa’azi ya yaɗa labarin.
Don haka wajibi ne malamai su riƙa hattara game da inda za su riƙa tantance yadda suke samun labari ko wasu muhimman bayanai, kuma su yi nazarin bayanan kafin su fitar da shi ga jama’a.
A wasu shekaru da suka gabata a Jihar Filato, an taɓa samun wata wasiƙa da wasu marasa son zaman lafiya suka riƙa yawo da ita ana yaɗa cewa, wata ƙungiyar addini ta rubuta cewa, za a kai hare-hare a wasu wurare mallakar mabiya wancan addini. Mutane da dama sun yarda da wannan labarin, duk da kasancewar bincike ya tabbatar da ba wasiƙar gaskiya ba ne. Har sai da manyan limaman addinin Musulunci da na Kirista suka shiga kafafen watsa labarai suna roƙon jama’a kan su yi watsi da wannan jita-jita.
Ire-iren waɗannan labaran suna da yawa, kuma suna cigaba da haifar da rashin jituwa da saɓani a tsakanin jama’a. Don haka ƙoƙarin da wannan ƙungiya ta Alƙalanci take yi wajen shiryawa malamai da fastoci bita da ilimantar da su yadda za su gane labari mai inganci da sahihan bayanai da za su yi amfani da su a karantarwar da suke yi wa jama’a. Hakan zai taimaka ƙwarai da gaske wajen samar da sahihan bayanai ga jama’a da kuma tsare mutuncin malamai da kimarsu a idon mabiya su.
Ya zama dole a yabawa Cibiyar Alƙalanci bisa ƙoƙarin da take yi na wayar da kan jama’a da ilimantar da masu ruwa da tsaki, ta yadda za a samar da tsaftataccen yanayi, inganta zaman tare, da kyakkyawan jagoranci a tsakanin jama’a.
Su kuma malaman addini, muna kyautata musu zaton za su yi aiki da abubuwan da suka koya kuma su wayar da kan jama’a kan illar yaɗa jita-jita da maganganun ƙarya marasa tushe waɗanda ba su dace a ji daga bakin su ba.
