14
Oct
Daga AISHA ASAS Akwai marubutan da mutuwarsu ke rufe wani shafi kawai na rayuwarsu, amma akwai waɗanda mutuwarsu ke sa duniya ta sake waiwayar irin tasirin da suka bari a duniyar littattafai. Ga marubucin Birtaniya Jeffrey Archer, labarin rasuwarsa a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, ya zo ne a daidai lokacin da yake gab da rufe dogon tafiyar da ya yi a matsayin marubuci. Archer ya rasu yana da shekara 86, kwana guda kafin a fitar da littafinsa na ƙarshe mai suna 'Adam and Eve'. Kamfanin buga littattafansa, HarperCollins, ya tabbatar da cewa marubucin ya mutu cikin kwanciyar hankali a…
