
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jimillar ‘yan Nijeriya guda 315 da suke cikin halin matsi a ƙasar Afirkata Kudu ne rukunin ƙarshe daga cikin waɗanda Gwamnatin Nijeriya take ƙoƙarin tabbatar da dawo da su gida bayan hare-haren ƙyamar baƙi da suka riƙa fuskanta a sassan ƙasar.
Ana sa ran jirgin ƙarshe da zai yi jigilar ‘yan Nijeriyar ya bar Afirka ta Kudu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda ake sa ran ya iso Filin Murtala Muhammed da ke Legas da mislain ƙarfe 6:30 na safe.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar wa manema labarai a ranar Talata.
A cewar ma’aikatar, ana aikin ne kaɗai ga waɗanda suka nuna buƙatar suna son su bar ƙasar bisa farmaki da suke fuskanta daga ‘yan ƙasar kudancin Afirkan da kuma lalacewar lamuran tsaro a wasu sassan Afirka ta Kudu.
Da fari, gwamnatin tarayyar ta yi jigilar ‘yan Nijeriya daga ƙasar ta amfani da jiragen sama guda huɗu da suka ɗebo ɗaruruwan mutane da hare-haren kwanan nan ya shafe su.
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta kuma bayyana cewa, jigilar da za a yi a gobe Laraba, za ta zama ta ƙarshe daga cikin shirin gwamnatin na kwaso ‘ya’yanta da ke fuskantar barazana a can, tana mai tabbatar wa ‘yan ƙasa ƙoƙarinta na bayar da kariya ga walwalarsu a ciki da wajen Nijeriya.
