25
Sep
An sauke farashin litar mai zuwa Naira 430 don amfanin 'yan acaɓa da matuƙa adaidaita-sahu da 'yan taksi a jihar Borno. Bayanai sun ce ƙaddamar da dogayen motoci guda 70 da gwamnatin jihar ta yi don rage raɗaɗin rayuwa inda jama'a kan biya N50, hakan ya sa sauran masu abubuwa na 'yan kasuwa a jihar kowa na neman matsaya. An ce wasu masu hannu da shuni a jihar suka bai wa gidajen mai a babban birnin jihar kwangilar sayar da fetur N430 kan kowace lita a maimakon N637. Bayanai sun ce masu hannu da shunin sun ɗauki wannan mataki ne…