Ci gaba da ba da tallafin wutar lantarki na kashi 85 na nuni da gwamnatin Tinubu ta al’umma ce –Idris

Daga BASHIR ISAH

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, ci gaba da ba da tallafin lantarki da kashi 85 da Gwamnatin Tarayya ke yi hakan ya ƙara tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta al’umma ce.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a lokacin da yake yi wa ‘yan jarida jawabi a Abuja.

Ta bakinsa, “Kwanaki kaɗan da suka gabata Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabon tsarinta don cigaban fannin lantarki mai ƙudurin samar da wadatacciyar wutar lantarki a faɗin ƙasa.

“Ɓangare mafi muhimmanci a tsarin shi ne, gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da ba da tallafin wutar lantarki na kashi 85 ga ‘yan Nijeriya masu amfani da wutar wanda hakan ke jaddada cewa gwamnatin ta al’umma ce.

“Yayin da ƙarin wutar lantarkin ya shafi kashi 15 ne kacal na ilahirin masu amfani da wutar lantarki a faɗin ƙasa,” in ji shi.

Tun farko, sai da Ministan ya taɓo bayani kan nasarorin da gwamnatin Shugaba Tinubun ta samu tun bayan da ya karɓi ragamar mulkin ƙasa a watan Mayun bara wanda suka haɗa da bunƙasa tattalin arziki da gina manyan hanyoyi da dai sauransu.