Gwamna Namadi ya dakatar da kwamishinansa kan zargin almundahana

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Gwamna Jihar Jigawa Umar Namadi, ya dakatar da Kwamishinan Harkokin Kasuwanci na Jihar, Hon Aminu Kanta, bisa zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Ana zargin Aminu Kanta da wawushe kuɗaɗen da gwamnatin jihar ta ware domin tallafa wa al’ummar Ƙaramar Hukumar Ɓabura da abinci a lokacin azumin watan Ramadan.

Bayanin dakatarwar na ƙunshene a cikin wata takardar sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Alhaji Bala Ibrahim Mamsa wadda aka raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar ta dakatar da Aminu Kanta daga muƙaminsa na Kwamashinan Harkokin Kasuwancin Jihar Jigawa saboda laifin da ake zarginsa da aikatawa har sai an kammala bincike a kansa.

Sanarwa ta ƙara da cewa, dakatarwar ta fara aiki ne nan take har zuwa lokacin da kwamatin bincike zai kammala bincikensa.

Sakataren ya bayyana cewa, wannan mataki da gwamnatin ta ɗauka tamkar tauna tsakuwa ce don aya ta ji tsoro. Yana mai cewa, hakan shi zai tabbatar da lallai da gaske gwamnatin take wajen hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba a ƙarƙashinta.