Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso barazana ce ga tsaro — ECOWAS

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta bayyana yunƙurin ficewar ƙasashen Nijar da Chadi da Burkina Faso daga cikinta a matsayin mummunan barazana ga harkokin tsaron yankin.

Kwamishinan harkokin siyasa, zaman lafiya da tsaro na ECOWAS, Abdel-Fatau Musah ne ya bayyana hakan a yayin wani zama mai taken: “Daƙile Matsaloli Ta Hanyar Haɗin Gwiwar  Masu Ruwa da Tsaki a Fannin Tsaro A Yankin da Abin Ya Shafa” wanda Ƙungiyar Tarayyar Turai tare da haɗin gwiwar Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci (NCTC) suka shirya a Abuja ranar Laraba.

A watan Janairu ne dai ƙasashen uku da sojoji ke jagoranta suka sanar da ficewarsu daga ECOWAS.

Sun ce sun fita daga ECOWAS ɗin ne saboda zargin ƙungiyar da zama barazana ga ’yan ƙasashensu.

Musah ya ce: “ Ficewar mambobin ECOWAS uku su kuma ƙulla kawancem Sahel ya dagula yaki da ta’addanci a yankin Afirka ta yamma.

“Matsayar ECOWAS a nan ita ce muna bukatar waɗannan ƙasashen su dawo a ci gaba da tafiya tare, kuma za mu yi duk abin da ya dace domin dawo da su.

“Muna buƙatar su, taken wannan taro namu shi ne haɗin gwiwa, haɗin gwiwa da abokan arziki domin yakar babban abokin gaba wato ta’addanci.”

Kwamishinan na ECOWAS ya ce, tuni ta’addanci ke barazana ga ƙasashen uku, yana mai cewa “Idan ba mu hada kai mun yaki wannan ba, dukkanmu za mu shiga matsala.”

Ya ce, ’yan ta’adda sun mamaye kusan rabin kasar Burkina Faso, akwai fargabar cewa Afirka da ma duniya baki daya za su iya shiga gagarumar matsala idan har aka bar ’yan ta’adda suka samu wurin zama mai kyau na kai hare-hare a Yammacin Afirka.

Ya ce, a yanzu haka ƙungiyar ECOWAS na shirin gudanar da wani taro domin tunkarar matsalolin da suka dabaibaye ƙasashen uku, da hanyoyin magancesu.

By Editor