Ɗaukar doka a hannu ke janyo faɗa tsakanin manoma da makiyaya – Alhaji Akote

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen ƙaramar hukumar Argungu Alhaji Hara Akote Badariya ya bayyana ɗaukar doka a hannu ne dalilin faɗa tsakanin manoma da Fulani makiyaya.
Ya yi wannan bayanin ne a wata hira da ya yi da waƙilin jaridar Blueprint Manhaja a garin Argungu.
Alhaji Akote Badariya ya ce tsakanin manoma da Fulani a ƙasar nan ba wanda ke iya raba su saboda ɗaya bai yi sai da ɗaya don haka suka tarar tun kakanni da iyaye, idan makiyaya suka yi ɓarna ko dai a yi sulhu tsakanin su ba sai an je ga hukuma ba ko kuma a je ga hukuma don shiga tsakani idan abin ya buwaya amma dai faɗa har ya kai ga kashe-kashe kam wannan bai dace ba.

Hasali ma saboda haka ne yanzu a ke tura ƙananan yara wajen kiwo saboda su sukan gudu idan suka ga mai gona da suka yi wa ɓarna amma babba kam ba ya gudu sai dai ya tsaya a yi faɗa da shi wanda shi ne ya yi sanadiyyar faɗa da aka yi a garin Gulma kwanan nan har aka rasa rayuka takwas wanda ba ƙaramin koma-baya ba ne.
Ya ja kunnen Fulani da su guji maganar ɗaukar fansa su bar wa Allah su jira su ga abinda hukuma za ta yi saboda ta sha alwashin ɗaukar matakin da ya dace ga duk wanda ke da hannu a cikin wannan kashe-kashen.

Ya ƙara da cewa yanzu Fulani sun zama ɗaya da mutanen gari saboda suna hira cikin gari har zuwa ƙarfe goma sha biyu na dare saɓanin inda aka fito inda tun ƙarfe biyar fulani ke baro cikin gari.
Ya kuma yi kira ga manoma da su daina ɗaukar doka a hannun su, su rinƙa kai rahoto ga hukumomin da ke kusa a duk lokacin da wani makiyayi ya yi musu ɓarna.

By ukarofi

Leave a Reply