04
Oct
Daga BELLO A. BABAJI Ana hasashen ƴan Nijeriya za su fuskanci matsalar ƙarancin man fetur na ba da jimawa ba sakamakon samun tseko da ƴan kasuwa ke fuskanta dakon fetur bayan da kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPCL ya rufe shafinsa na sayen mai. Mai magana da yawun ƙungiyar ƴan kasuwar fetur ta Ƙasa, Chinedu Okadike ya faɗi hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba inda ya ce ƴan kasuwa na da tikiti 2,000 na sayen fetur da adadinsa ya kai lita 45,000. Ya ce, rufe shafin ka iya shafar yalwar mai a cikin al'ummar Nijeriya, ya na mai cewa…