26
Mar
Tare da CHIROMA AMINU ASID Sau da dama mutane na iya fuskanta wani yanayi na saurin jin fitsari bayan sahur. Hakan yana faruwa ne, saboda wasu dalilai na halitta da ɗabi’a, kamar haka:- Shan ruwa da yawa lokaci guda: Idan mutum ya sha ruwa da yawa a lokaci guda, ƙodojinsa za su riƙa tace ruwan da wuri. Hakan na sa yawan fitsari. Shan kayan sha masu ‘caffeine’: Shan abubuwan sha masu ƙarfafa fitsari (Diuretics), wasu nau’in abinci ko abin sha na iya sa fitsari ya ƙaru. Wannan ya haɗa kayan sha masu ‘caffeine MM’, kamar a shayi da kofi, kayan…