Rahoto

Duniyar marubutan Hausa ta girgiza bisa rasuwar Marubuci Bello M. Bello

Duniyar marubutan Hausa ta girgiza bisa rasuwar Marubuci Bello M. Bello

Daga ADAMU YUSUF INDABO a Kano Fitaccen matashin marubucin littattafai da fina-finan Hausa, kuma jarumi a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, wato Bello M. Bello ya koma ga Mahaliccinsa a daren Talatar da ta gabata (26, 10, 2021). Marigayi Bello M. Bello ya rasu ne a dalilin ciwon ciki da ya kama shi jim ka]an bayan ya yi sallar Magriba, kuma nan take, ya ce ga garinku nan. Ya rasu a gidansa dake cikin garin Ringim ɗin jahar Jigawa, kuma an yi jana'izarsa a washegari ranar Laraba 27, 10, 2021 da misalin ƙarfe takwas na safe. Marigayi Bello M. Bello,…
Read More
Yadda ƙabilar Toraja ke daraja gawa fiye da mutum mai rai

Yadda ƙabilar Toraja ke daraja gawa fiye da mutum mai rai

A wannan mako, jaridar Manhaja ta kewaya duniya, inda ta yada zango a ƙasar Indonesiya da ke yankin Asiya. A yau filin namu ya yo tattaki na musamman ne zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, inda mu ka yi nazarin al’adar wata ƙabilar mai suna Toraja. Wani abu mafi ɗaukar hankali ta yadda har idon duniya ya ɗarsu a kan waɗannan al’umma shi ne yadda su ke tafiyar da sha’anin gawa ko kuma mu ce mamaci. Su dai waɗannan mutane su na rayuwa ne a cikin duwatsun da ke Kudancin Sulawesi na Ƙasar Indonesia, Kalmar ‘Toraja’ ta samo asali daga yaren…
Read More

Matsalolin ilmi a Jihar Kano

Gwamna Ganduje Daga FATUHU MUSTAPHA Ilmi na cikin vangarorin rayuwa da ya zamewa ɗan Adam tilas ya ba shi kulawa ta musamman. A yau Ƙasar nan tana fuskantar manyan matsaloli kama daga matsalar tsaro da a kullum ke ƙara ta'azzara, zuwa matsalar fatara da talauci, lalaci da jahilci da kuma karyewar tattalin arzikin ƙasa, wanda a ka fara sa ran zai iya farfaɗowa nan da wasu lokuta masu zuwa. Babu inda matsalolin nan suka fi nunawa kan su irin a Arewacin Nijeriya. Inda anan ne aka fi yawan yaran da basa zuwa makaranta, yawan yaran da basa cin jarabawar gama…
Read More
Samar da ilimi da cigaban rayuwa: Yadda Abdulnaseer Bobboji ya taka rawar gani a Jalingo

Samar da ilimi da cigaban rayuwa: Yadda Abdulnaseer Bobboji ya taka rawar gani a Jalingo

Daga MUKHTAR YAKUBU a Jalingo A rayuwar duniya ta wannan lokaci, babu wani abu da a ke buƙatar ɗan Adam ya samu kamar ilimi na zamani da kuma na addini. Wannan ya sa ƙasashen da suka cigaba sika ɗauki ɓangaren ilimi da muhimancin gaske ta yadda su ke ba shi kyakyawar kulawar da ta dace, domin kuwa ana samun al'umma masu cigaba ta hanyar bunƙasar iliminsu ta kowanne ɓangare. Domin masana sun ce babu wata al'umma da za ta ci gaba tana cikin duhun jahilci, don haka ne duk wata gwamnati walau ta tarayya ko ta ƙaramar hukuma da ta…
Read More
Masu garkuwa da mutane sun shata daga a junan su: Sama da mutum ɗari sun mutu

Masu garkuwa da mutane sun shata daga a junan su: Sama da mutum ɗari sun mutu

Daga FATUHU MUSTAPHA A ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na yamma ne wani gungun masu garkuwa da mutane suka nemi kutsa kai cikin garin Illela na Ƙaramar Hukumar Safana da ke Jihar Katsina. Wannan kutse ya janyo musayar wuta tsakanin su da wani gungun masu garkuwa da mutanen, inda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum ɗari, ciki kuwa har da mata da yara ƙanana. Rahotanni sun bayyana cewa wannan rikici ya faru ne tsakanin gungun Mani sarki da na Ɗanƙarami wanda ke da goyon bayan Gungun Abu Rada. Shi dai Sarki Mani wanda a da tsohon mai garkuwa…
Read More