Kafa makarantun boko na farko a Ƙasar Hausa

Daga SADIQ TUKUR GWARZO

Kafin a gabatar da ilimin boko a Jihohin Arewa, sai da Gwamna Lugga ya sa aka yi bincike aka gano yawan makarantun allo da ake da su, da yawan almajiransu. A cikin wani kintaci-faɗi an gano cewa a farkon ƙarni na ashirin, akwai makarantun allo guda 25,009 masu yawan ɗalibai 218,618 a garuruwan jihar Arewa.

Ganin ƙarfin ilimin addininin Musulunci, sai Gwamna Lugga ya ga cewa ba daidai ba ne a gabatar musu da ilimin boko kamar yadda ake tafiyar da shi a Ingila. Mun dai riga mun sani tun wajen shekarar 1900 aka buɗe makarantun Ilimin zamani na farko a Lakwaja da Wusasa ta zariya a ƙarƙashin ƙungiyar Mishan. Amma kafin a buɗe ta gwamnati dole ne sai an yi ‘yan gyare-gyare ta yadda zai dace da wannan al’umma.

Wannan shine ya sa a cikin 1909 Gwamna Lugga ya zaɓi wani Bature wanda yake ɗaya daga ma’aikatan sa mai suna Sir Hans Vischer, wanda ake yi wa laƙabi da Ɗan Hausa saboda ya ji Hausa qwarrai, aka naɗa shi jami’in ilimi a Jihar Arewa, aka tura shi ya ziyarci Misira da Sudan (watau ƙasashen Musulmi) da Gwalkwas (Ghana) (watau Ƙasar Africa baqar fata wadda ta jima da fara yin ilimin zamani), ya yiwo nazari game da irin tsarin da suke bi wajen gudanar da ilimi a ƙasashen su don ya gabatar wa jihar Arewa wanda yafi dacewa. Da Hans Vischer ya dawo a wannan shekara ta 1909, sai ya buɗe makarantar boko ta gwamnati ta farko a wurin da ake kira Nassarawa, a wajen Birnin kano. Ita wannan ita ce makarantar elementare ta farko wadda aka fi sani da suna Makarantar Ɗan Hausa. Kafin a fara koyarwa a cikinta, sai Sir Hans Vischer ya zavi ƙwararrun malaman Arabiyya ya zuba su a makarantar don su taya shi wajen koyarwa.

An tsara manufofin ilimi a makarantar kamar haka:-

(a) Koyar da waɗanda za su zama malaman makaranta a wurare daban-daban na jihar Arewa.

(b) Bai wa ’ya’yan sarakuna ilimin gudanar da mulki a hanyoyin zamani.

(c) Koyar da ilimin ayyukan gwamnati ga waɗanda suka nuna ƙwazo don Turawa su ba ’yan ƙasa damar gudanar da wasu ayyuka na gwamnati.

Muhimmin abin sha’awar shi ne, da hausa ake koyar da fannoni daban-daban a makarantar, ba da Turanci ba. Ana koyar da Turanci amma a matsayin fannin harshe ne kawai, ba harshen koyar da fannonin ilimi ba. Wasu daga cikin fannonin da ake koyarwa su ne karatu da rubutu da lissafi. Sai tarihi da labarin ƙasa. Sai kuma sana’a domin akwai malaman sana’a da na Arabiyya a makarantar.

A shekarar farko ta 1909, ɗaliban makarantar su talatin (30) ne waɗanda suka zo daga garuruwa daban-daban na lardunan Arewa. A shekara ta 1910 ne aka zavi sir Hans Vischer ya zama Daraktan Ilimi a jihar Arewa, Kano kuma ta zama hedikwatar ilimi a wannan lokacin. A cikin ’yan shekaru kaɗan sai makarantar ta bunƙasa. Misali, a shekarar 1913, kaɗai, ɗaliban makarantar Ɗan Hausa ta kano sun kai yawan 208 waɗanda suka zo daga larduna daban-daban kamar haka:-

Kano 59

Neja 49

Muri 25

Barno 17

Binuwai/filato 13

Kontagora 13

Nassarawa 12

Yila 11

Zaria 7

Ilori 6

Sakkwato 6.

A tsakankanin shekarar 1914 zuwa 1919 an buɗ”e makarantun ilimin boko a wurare daban-daban na jihar Arewa. Ganin makarantun Ilimin boko suna daxa yawaita, sai hedikwatar ilimi ta tashi daga Kano ta koma Kaduna domin kulawa da makarantun larduna na gwamnati su goma sha ɗaya, da makarantun mishan su 114 a Jihar Arewa. Bayan makarantun larduna sun samu, matsalar da ta fuskance su ita ce ta littattafan karantawa..” (sannu a hankalinsai aka soma fuskantar su).

Sadiq Tukur Gwarzo ya ciro daga littafin HAUSA A RUBUCE: TARIHIN RUBUCE-RUBUCE CIKIN HAUSA Na Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya (Allah ya rahamshe shi amin).