Kano: Hisbah ta kama maza da mata 20 suna wanka tare

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama wasu mutum 20 da suka haɗa da maza da mata bisa laifin yin wanka tare.

Jami’an Hukumar ɓangaren ‘Operation Kau Da Baɗala’ sun kama su ne a wani wurin shaƙatawa da ke kan titin Ring Road sakamakon ƙorafin da mazauna yankin suka yi.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahidin Aminuddin Abubakar, ya ce laifin ya sab’ɓa wa dokar Hisbah domin ta hana haɗa jinsin biyu a cikin ruwa domin yin wanka.

Ya nuna damuwarsa kan lamarin, wanda a cewarsa, za a iya maye gurbinsa da wani aiki mai fa’ida da za a samu lada a wajen Ubangiji.