Hajji 2024: Jirgin farko ya bar Nijeriya ɗauke da maniyyata 422

Spread the love

Yayin da Hajjin bana ya ƙarato, Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta fara jigilar maniyyatan bana zuwa ƙasa mai tsarki.

A ranar Laraba hukumar ta ƙaddamar da jigilar inda ta fara da maniyyatan jihar Kebbi su 422 da jami’ai 7.

Jirgin Flynas mai lamba XY8002 shi ne ya kwashi maniyyatan zuwa birnin Madina da misalin ƙarfe 4:54.

Daga adadin naniyyatan, 269 maza ne, sannan 153 mata.

By Editor