Mata A Yau

Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

Soyayyata ga kayan gona ya sa na tsunduma sana’ar kayan gwari – Ummu Sodeeq

"Samarin yanzu ma sun fi son mace mai sana'a" Daga AISHA ASAS Mai karatu yau fa mun zo da abinda ba ku yada gani ba, mace da ta tabbatar da zancen ba sana'ar da namiji zai yi da mace ba zata iya ba matuƙar ta sa wa ranta za ta iya. A daidai wannan lokacin da mata suka miƙe, suka yi tarayya wurin kama sana'ar kayan qawa na mata da maza, kama daga tufafi, takalma zuwa huluna, gyale da sauransu, waɗanda su ne sana'oin da aka cika ganin mata na yi. A cikin haka ne, aka samu wata matashiya da…
Read More
Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

Wacce ta ce jari ya hana ta sana’a, ba ta tashi yi ba – Hafsat Adamu 

"Ilimin 'ya mace har mijinta ke amfana" Daga AISHA ASAS  Mai karatu barkan mu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Kamar kowanne mako, shafin Gimbiya na yi maku tanadi na musamman wanda muke da tabbacin mata za su amfana ta vangarori da dama, ya Allah ya zama ƙwarin gwiwa ga wasu, wasu ya zama ilimi da zai taimaka masu wurin miƙewa neman na kai, yayin da yake zama allon kwaikwayo don saisaita rayuwarsu bisa ga turba da za ta tsirar da su. A wannan satin, mun samu baƙuncin wata matashiya da ta ɗauki sana'a da muhimmanci, mai sana'ar 'yankunne ce,…
Read More
Mu kula da rayuwar ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Mu kula da rayuwar ’ya’ya mata masu shaye-shaye

Tare Da ABBA ABUBAKAR YAKUBU Matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa ba baƙon abu ba ne, musamman ma ga ’y’ya maza, inda yake da mamaki da ɗaukar hankali shi ne a ga ’ya mace budurwa, bazawara ko matar aure tana bulayi cikin maye ko a ga tana ɗaga kwalba ana shewa da ita, babu ma dai kamar yarinya ’yar musulma kuma bahaushiya ko ’yar Arewa, da ake kyautata mata zaton ta taso a gidan tarbiyya, kunya da ƙyamatar irin waɗannan halaye marasa kyau. Ba lallai ya zama abin kunya ga matan bariki ko masu zaman kansu da aka fi…
Read More
Ƙarfafa wa mace gwiwa ta hanyar yaba kwalliyarta

Ƙarfafa wa mace gwiwa ta hanyar yaba kwalliyarta

Tare Da AMINA YUSUF ALI Assalamu alaikum sannuku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako za mu tattauna akan irin yawan ƙorafi na mijin bahaushe yake yawaita yi na cewa matarsa ba ta kwalliya da makamantansu. Su ma kuma matan Hausawan kana tuntuɓarsu, za su ce ai su ma idan sun yi ba a yabawa. Sai dai masu iya magana sun ce, Bahaushe ya ce, idan an bi ta varawo, to sai a bi ta ma bi sawu. Sannan kuma idan ɓera da sata, to daddawa ma fa akwai ta da mugun wari. Abin…
Read More
Amfanin ayaba ga matan aure

Amfanin ayaba ga matan aure

Daga AISHA ASAS Mai karatu sannunmu da sake saduwa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja. A wannan satin da yardar mai dukka, za mu taɓo ɓangaren ni'imar jikin mace da za a iya samu ta ɓangaren ayaba. Na san wasu za su ga abin tamkar almara, kasancewar da yawa ba su ɗauke ta a matsayin komai ba face ƙwalama. Sai dai ayaba kamar wasu daga cikin 'ya'yan itace 'yan'uwanta, tana taka muhimmiyar rawa a ƙarin ni’ima ga mata. Ayaba na ɗaya daga cikin kayan qarin ni’ima na mata, yawan cinta, musamman idan kina haɗa ta da madara zai ba ki…
Read More
Uwa: Makarantar farko ga ‘ya’yanta

Uwa: Makarantar farko ga ‘ya’yanta

Daga AISHA ASAS Annabin rahma ya ce, “daɗin duniya na tattare da samun mace ta gari” domin da mace ta gari ce za ka samu kwanciyar hankali, za ka samu natsuwa tare da biyan buƙatun yau da kullum, ga uwa uba samun ‘ya’ya na gari. A yau darasinmu na iyali zai karkata ne kan maza, tun daga samari da ba su yi aure ba, zuwa magidanta da ke shirin ƙarin aure. Domin dai kuskuren daga wurin ku ne ya samo asali. Da yawa daga maza abin da suka fi kallo a matar da za su aura ba shi da tasiri…
Read More
Babu amfanin samun mace in har ba za ta taimaki mijinta ba – Jiddah Haulat Nguru (2)

Babu amfanin samun mace in har ba za ta taimaki mijinta ba – Jiddah Haulat Nguru (2)

"A wannan zamani sana'a kamar dole ta zamewa 'ya mace" Daga AISHA ASAS A satin da ya gabata, mai karatu idan bai manta ba, mun ɗauko fira da matashiya Jiddah Haulat Nguru, inda ta fara bayyana mana tarihi da kuma irin sana'ar da take yi, wadda ta tabbatar mana ana cin kasuwarta ne a kafafen sadarwa, sannan ta yi mana bayanin yadda ta fara, da hanyoyin da take bi don siya da siyar da kayanta a kafafe kamar Fesbuk, WhatsApp da sauransu. A wannan satin, za mu ɗora ne daga inda muka tsaya. Kamar yadda muka sanar, baƙuwar tamu za…
Read More
Zuwa ga ‘yan mata: Binciken aure ba aikin iyaye ne kaɗai ba

Zuwa ga ‘yan mata: Binciken aure ba aikin iyaye ne kaɗai ba

Tare Da AMINA YUSUF ALI Barkanmu da sake haɗuwa a wani sabon makon a shafinku na zamantakewa na jaridarku mai fari jini ta Manhaja. A wannan mako za mu tattauna a kan yadda budurwa ko bazawara za ta taya iyayenta bincike a kan mijin da suka daidaita, kuma suke fatan su raya sunnar Annabi SAW ta auren juna da za su yi. Menene bincike a aure? Kamar yadda muka sani a ƙasar Hausa, da wuya a ce an yi aure ba tare da iyayen yarinya sun yi bincike a kan wanda ya zo neman auren ɗiyarsu ba. Wato za su…
Read More
Ku ba wa iyalanku kariya daga cutar mashaƙo

Ku ba wa iyalanku kariya daga cutar mashaƙo

Daga AISHA ASAS Kamar yadda yake haƙƙi da ya rataya kanka maigida na daga ci da sha ga iyalanka, haka ya kasance haƙƙi gare ka ka ba wa iyalanka kariya daga curutukan da ka iya yiwa iyalanka lahani. Ba ma maigida kawai ba, a matsayinki ta uwa mai kula da sha'anin iyalinta ke ma ya kamata ki kula tare da mayar da hankali wurin ganin curutukan nan na zamani sun tsallake gidanki. Wannan ne ya sa yake da matuƙar muhimmanci samun ilimi kan kowacce irin cuta da ke yaɗuwa, wanda hakan zai ba ku dama, wurin ba wa 'ya'yanku da…
Read More
Ta yaya za a iya magance warin gaba

Ta yaya za a iya magance warin gaba

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Manhaja. A satin da ya gabata, mun tavo bayyani kan dalilan da ke haifar da warin gaban mace, wanda muka tabbatar ba halitta ba ce. A wannan makon, da yardar mai dukka, za mu kawo wasu daga cikin ababen da uwar gida za ta yi don kawar da warin gaba, sai dai kamar yadda muka yi bayanin ababen da ke haifar da warin na gaba, zan so uwar gida ta fara da haddace su, ya zamana ta kauce wa dukka hanyoyin na samuwar warin kafin ta…
Read More