Matan aure barka da Ramadan!

Tare da AMINA YUSUF ALI

Zuwa ga matan aure da suke bibiyar wannan shafinmu na Zamantakewa mai zuwar muku kowanne mako a jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. A wannan mako shafin na matan aure ne. Duba da watan da muke ciki na Ramadan mai albarka. ‘Yanuwana mata barkanmu da warhaka da fatan kuna cikin ƙoshin lafiya. Allah ya karɓi ibadunmu ameen. To a wannan mako mun kawo muku wasu dabaru ta hannun ƙanwata Sakina Yazid yadda uwargida da amarya za su kauce wa wahalar azumi, ko ma na ce za su rage wahalar azumi.

A wannan yanayi da muke ciki na haɗuwar zafin gari da kuma ƙishin azumi, sannan kuma ki tunkari wuta gadan-gadan a lokacin da ya fi kowanne wahalar azumi. Wato idan rana tana kusa da faɗuwa azumi ya fi wahala kuma ƙishin ya fi ta’azzara, ga wuta da zafi.

Daga zarar wannan zafin na wuta ya daki jikinki kika fara babbakewa sai ka ce balangu, sai ma ki rasa inda za ki saka kanki saboda tsananin ƙishi da wahala. Yanzu ga wasu dabarun da muka kawo muku saboda kauce wa haka:

1) Ki tsara wasu abubuwan girkinki kafin rana ta ɗauki zafi. Misali kamar jajjage da yanke-yanke. Idan kwaɓi ne ma ki yi kwavinki, idan wake ne ki dafa shi tun wuri, so samu ma ki haɗa lemon buɗa baki ki sanya a firji. Duk wani abin da zai yiwu ki yi shi da safe kafin 12 tun ba ki fara jigata da azumin ba. Sai ki bari sai ƙarfe huɗu ma za ki tunkari madafi, kuma ki gama a kan lokaci.

2) Bayan kin kammala waɗancan abubuwa da aka lissafa a sama, sai kuma ki samu ki ɗan kwanta ki huta ko da bayan azahar ne. Ko hutu kika samu na aƙalla minti 30 ya isa.

3) Idan lokacin shiga madafin ya yi, ki sanya kaya marasa nauyi waɗanda za ki sha iska.

4) Ki yi ƙoƙarin kammala girkinki kafin lokacin buɗa baki ya yi. Hakan zai ba ki damar samun sararin ɗan watsa ruwa a jikinki kafin a kira sallah.

Ki nemi dukkan taimakon da za ki iya kamar ki samo mai aiki wacce za ta taya ki, ko ƙanne, ko yaranki waɗnda suka tasa. Kowa ki ba shi abinda zai iya taimakawa da shi. Aikin azumi yana da yawa.

Ki dinga shan ruwa sosai lokacin buɗa baki da sahur, sannan ki tabbatar kina ɗan samun hutu. Hakan zai taimaka sosai. Sannan ki duƙufa addu’ar neman ɗauki daga Allah.

Sanan kuma dukka a tsarabar watan Ramadan mun kawo muku wasu girke-girke don canza tukunyar iyakti sabida wata ne na marmari da buƙatar abinci lafiyayye. Ga wasu girke-girke masu sauƙi:

 1. Tsiren tukunya
  Kayan da ake buƙata:
  Naman sa, ƙuli-ƙuli dakakke mai Maggi, gishiri, barkono, citta, Onga, curry a cikin sa da dai sauran kayan kamshi da kuke so), mangyada, albasa, ruwa.

Da farko dai za a samu ƙuli-ƙuli kuli mai kayan haɗi a ciki, sai ruwa da albasa a yanka. Sai a tafasa nama tare da haɗin su Maggi da kayan ƙamshi ya dahu luguf har ya tsotse ruwan, sai ai ta juya naman har ya fara kamawa kadan. Sai a juye shi.

 1. Dambun kus-kus:
  Kayan da ake buƙata:
  Kus-kus, zogale, lawashi, gyada, kayan miya, magi, ruwa, da sauransu.

Yadda ake yi:
Za ki zuba kus-kus a roba, sai ki zuba ruwa ɗan dai-dai. Ki wanke zogale da lawashi.
Daga nan sai ki sa gyadar da aka daka a kai, za ki jajjaga tatasai, atargu albasa ki zuba a kai.

Daga nan za ki sa magi da kayan ƙamshi sai ki gauraya. Daga nan za ki zuba kus-kus ɗin a cikin kwalanda, ki rufe shi da foil paper da murfin tukunya na tsahon mintuna 30. Za ki buɗe ki sake juyawa sai ki rufe. Ki nemi albasa ki soya da man gyada ya ɗan yi ja kaɗan.

Sai ki sauke kus-kus ɗin din ki zuba a roba ki juye man gyadan a kai ki jujjuya, sannan ki sake maida shi wuta na tsahon mintuna. Dambu kuma ya yi sai ki sauke. Za ki iya yayyanka masa albasa, attaruhu da tumatir da ƙwai a kai. Ko a sa yaji ko miyar jajjage da nama da sauransu.

 1. Abin sha na kwakwa da dabino
  Abinda ake buƙata: Kwakwa, dabino, madara da suga, filebo.

Yadda ake yi:
Da farko za ki samu kwakwarki, ki goge bayanta da abin gurza kuɓewa, sai ki samu dabinonki ki cire ƙwallyen tas ki haɗa da kwakwar ki wanke su ki sa a bilenda ki markaɗa su. Sai ki tace ki saka sukari da madara da fillebo. Wannan haɗi yana kuma ƙara wa mace lafiya da kuma ni’imar. Musaman lokacin azumi da ni’imar mace takan yi ƙasa sosai.

To a na zan dakata. Allah ya karvi ibadunmu da addu’o’inmu. Sai wani makon idan Allah ya kai mana rai.