A kawo ɗauki don magance tsadar kuɗin zuwa aikin Hajjin Bana

Daga ABUBAKAR IBRAHIM

A kowace shekara, al’ummar Musulmi suna gudanar da aikin Hajji domin cika ɗaya daga cikin shikashikan addininsu guda biyar. Abu ne wanda kowane Musulmi ke son cimmawa, aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa, yayin da kuma wani mai ƙumbar susa yake da burin ya sake komawa ya ƙara yi. Duk da haka, wanda ke da hali ne kaɗai aka wajabta wa yin wannan tafiya zuwa ƙasa mai tsarki don sauke farali.

A Nijeriya, tuni shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin shekarar 2024 suka kankama. Sai dai kuma ana ta samun wani babban ƙalubale, musamman na kuɗin tafiya aikin na maniyyata. Duk da ƙoƙarin da Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) take yi na ganin an shawo kan tsadar kuɗin tafiya Hajjin bana, farashin ya yi tashin gwauron zabi wanda ba a taɓa ganin irinsa a baya ba. Lamarin ya jefa maniyyata cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi da tsananin ruɗani.

Duk da ce-ce-ku-cen da ake yi game da ƙarin kuɗin, matsalar ta samo asali ne daga wasu manyan abubuwa guda biyu, su ne hauhawar farashin Dalar Amurka da kuma jinkiri ko ƙin biyan kuɗin aikin Hajji kan lokaci daga maniyyata.

Idan an tuna, tun da farko sai da hukumar NAHCON ta ƙayyade mafi ƙarancin kuɗin ajiya na aikin Hajjin bana a kan naira miliyan huɗu da rabi (N4.5m), aka ce za a faɗi farashi na ƙarshe bisa la’akari da farashin Dala a lokacin da za a kammala lissafa kuɗin. Saboda sauyin farashin Dala, ya zama tilas hukumar ta yi ƙari kan farashin ta na farko.

Ƙarin da aka yi dai sakamakon faɗuwar darajar Naira ne. Duk da ƙoƙarin da Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi ya yi na ganin farashin zuwa aikin Hajjin bana bai canza ba, an buƙaci maniyyata da su biya naira 4,899,000 ga waɗanda suka fito daga Kudu, waɗanda suka fito daga Arewa kuma naira 4,699,000, sannan naira 4,679,000 ga waɗanda suka fito daga yankin Yola da Maiduguri.

Matsalar da Nijeriya ta kwashe watanni tana fama da ita na canjin kuɗaɗen waje ya sa tilas hukumar ta nemi waɗanda suka biya kuɗin ajiya na kimanin naira miliyan 4.9 da su cika naira 1,918,032.91, daidai da farashin kuɗaɗen waje na yanzu. Hakan ya sa adadin kuɗin da masu niyyar zuwa aikin Hajjin za su biya ya zama naira miliyan 6.8 ga ‘yan ajiya. Su kuwa sababbin masu son biyan kuɗin za su biya naira 8,225,464.74 daga maniyyata daga Arewa, yayin da maniyyatan Kudu za su biya naira 8,454,464.73. Kuma hukumar ta ce ana buƙatar a kammala biyan waɗannan kuɗaɗen kafin ƙarfe 11:59 na dare a ranar 28 ga Maris, 2024.

Hukumar NAHCON ta yi ƙoƙari da dama wajen ganin maniyyata sun samu sauƙin farashi a bana. Misali, a farkon wannan shekarar shugaban hukumar ya jagoranci tawagar jami’ansa zuwa ƙasar Saudiyya inda suka tattauna da masu gidajen haya da otal-otal da motocin haya a garuruwan Makka da Madina da Masha’ir don su rage kuɗi ga maniyyatan Nijeriya, kuma sun samu matuƙar nasarar hakan. Tattaunawar ta haifar da raguwar farashin jirgi da masauki da sauran su. In da ba domin zuwan da suka yi ba, to da kuɗin zuwa Hajji da ake magana yanzu ya zarta haka.

Duk da matakan ragin kuɗaɗen da NAHCON ta ɗauka da suka haɗa da neman tallafin gwamnatocin jihohi da masu hannu da shuni ga alhazan su, da kuma shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya ta yi, gazawar maniyyatan wajen cika wa’adin da aka bayar na biyan kuɗin aikin Hajjin da aka ƙara shi ma ya haifar da ƙarin kuɗin zuwa aikin Hajjin bana. Rashin biyan cikakken kuɗi a kan lokacin da aka tsara ya haifar da tsawaita wa’adin, kuma yayin da aka tsawaita wa’adin, farashin kuɗaɗen waje na hauhawa. Hakan ne ya sa kuɗin aikin Hajjin ya ƙaru.

Ba shakka, ƙarin kuɗin aikin Hajji ya zama babban ƙalubale ga maniyyatan Nijeriya a bana. A halin da ake ciki, akwai alamun da yawa daga cikin maniyyatan da suka biya kuɗin ajiya ba za su iya biyan cikon naira miliyan 1.9 da ake buƙata ba, yayin da su kuma sababbin biya da yawansu sai dai ido, musamman a cikin taƙaitaccen wa’adin da NAHCON ta bayar. Hakan zai sa maniyyata su rasa damar zuwa Saudiyya gaba ɗaya.

Don haka, ya zama wajibi ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da masu hannu da shuni da su shigo cikin al’amarin, su ba da tallafi don sassauta nauyin da ke kan maniyyatan, tare da ɗaukar matakan da za su sa maniyyata na nan gaba su samu sauƙin yin wannan tafiya mai alfarma. Kada a naɗe hannu a zuwa wa matsalar ido, musamman a cikin wannan taƙaitaccen lokaci.

Abubakar Ibrahim ɗalibin digiri na biyu ne a Sashen Koyon Aikin Jarida a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya