Xavi ya yi amai ya lashe kan batun barin Barcelona

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Kocin Barcelona, Xavi Hernandez ya sauya shawararsa na barin Barcelona a ƙarshen kakar wasa ta bana kuma zai ci gaba da zama koci bayan tattaunawa da shugaban kulob ɗin, Joan Laporta, da shugabannin ƙungiyar a ranar Laraba.

An ruwaito Xavi ya gana da shugaban ƙungiyar, Joan Laporta da daraktan wasanni, Deco, a daren Laraba.

Bayan taron ya sauya ra’ayi kuma ya amince da sharuɗɗan ci gaba da jagorantar ƙungiyar ta LaLiga.

Ƙwararre a harkar wasan ƙwallon aafa Fabrizio Romano ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Romano ya rubuta: Xavi ya yanke shawarar canja ra’ayinsa ya zauna a matsayin kocin Barcelona!

“Bayan taron na daren ranar Laraba, Laporta ya nace cewa zai zauna, Xavi ya amince da sharuɗɗan Barca kuma zai ci gaba da zama koci.

Xavi, a watan Fabrairu, ya sanar da cewa zai bar Nou Camp a ƙarshen kakar wasa ta bana.