30
Nov
Robert Lewandowski ya zama ɗan wasa na uku da ya zura ƙwallaye 100 a gasar kofin zakarun Turai yayin da Barcelona ta lallasa Stade Brestois da 3-0 a wasan da suka fafata ranar Talata. Cristiano Ronaldo ne kawai mai ƙwallaye 141 da Lionel Messi mai 129 suka fi ɗan wasan mai shekaru 36 a yawan ƙwallaye na gasar zakarun Turai. Lewandowski ya zura ƙwallonsa ta 100 a minti na 10 da fara wasa, kuma shine ya ci ƙwallye biyu cikin ukun da ƙungiyar ta yi nasara. Dani Olmo kuwa ya ci wa Barcelona ƙwallonsa ta farko a gasar cin kofin…