Birnin Leverkusen ya bai wa ɗan Nijeriya, Boniface, shaidar zama ɗan ƙasa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Majalisar Birnin Leverkusen ta bai wa Victor Boniface, Nathan Tella da sauran zakarun gasar Bundesliga takardar shaidar zama ɗan qasa na girmamawa.

A ranar Lahadi Bayer Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga ta farko bayan da ta lallasa Werder Bremen da ci 5-0 inda Victor Boniface ya zura ƙwallon farko sannan kuma ya taimaka aka zura sauran ƙwallayen.

Victor Boniface yana ɗauke da fasfo na Nijeriya, yayin da Tella baya ga koren fasfo ɗinsa kuma yana da fasfo na ƙasar Birtaniya kamar yadda iyayen Nijeriya suka haife shi a Ingila.