Iran ta rama harin Isra’ila a Damaskas?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Babban labarin da ke ɗaukar hankalin duniya a yanzu shi ne harin da ƙasar Iran ta kai da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila. Da ma an yi wa duniya kirari da “Duniya mai yayi” in za ka ga a na batun wani sai kwatsam a jingine a shiga wani sabo.

Daga bara zuwa bana an ga yadda a ka yi labarin fitinar Sudan tsakanin Janar Abdelfatah Burhan da Hamdan Hameti Daglo bayan an fara gajiya da harin mamaye Yukrain da Rasha ta yi. Ga batun fitinar Yaman tun 2014 bayan ‘yan tawayen houthi sun ƙwace gwamnatin birnin San’a’a.

Maganar ta yi sanyi ita ma biyo bayan dawo da hulɗar jakadancin Saudiyya da ke mara wa zaɓaɓɓiyar gwamnatin Yaman ta birnin Aden baya da Iran mai mara wa ‘yan tawayen Houthi baya. Yanzu a na batun yaqin Gaza ne, inda a lokaci guda Isra’ila ke kai hari kan muradun Iran a Sham da Lebanon.

A sanadiyyar hare-haren na Ƙasar Isra’ila har ta kashe manyan jami’an Iran a ofishin jakadancin ta da ke birnin Damaskas. Cikin mutanen 7 har da manyan jami’an soja. A bisa al’ada Isra’ila kan kai hari ta kwana lafiya kuma ko a yanzu ma ta na cewa ta na nan daram don yadda ta ke da ƙarfin makamai da goyon bayan manyan ƙasashen duniya.

Ni da na ga harin da Isra’ila ta kai Damaskas ban ɗauka sabon abu ba ne don dama ta sha kai irin waɗannan hare-haren. Daga bisani da a ka yi bayanin ya shafi ofishin jakadanci da hakan ya keta haddin dokokin duniya sai na fahimci akwai bambanci.

Ƙarin tunani kuma a nan shi ne shin yaushe Allah ya taimaki Sham ta daina zama fagen yaƙi? Manyan ƙasashen duniya masu hamayya da juna sun maida Sham wajen raba raini da sunan kare wani vangaren yaƙin wa imma sashen gwamnatin Bashar Al’Asad ko na ‘yan tada kayar baya na ƙasar.

Haka za ka ga a na loda gawawwakin mutane a mota kamar mangalar yashi. A irin wannan yanayi ai za a iya fakewa da cewa akwai mayaƙan wasu ƙasashen a Sham da ke barazana ga Isra’ila don haka tamkar Isra’ila na kare kan ta ne. Don Isra’ila ta auna wani mayaƙi musamman na Iran a Sham ko a Lebanon ai hakan kawar da ‘yan ta’adda ne shi ya sa ma wasu ƙasashen ke gargadin Iran da sam kar ta ɗau wani mataki na ramuwar gaiya kan Isra’ila.

A kan zargi Iran da ɗaukar nauyin wasu mayaƙa da ke aiki a wasu ƙasashe a madadin ta kamar misalin cikin Sham, Lebanon, Iraqi da Yaman. Ma’ana ko da ba a ga Iran kai tsaye na yaki ba ta bayan gida ko ta ƙarƙashin ƙasa ta na yin hakan. In an tuna zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, Amurka ta kai harin jirgi marar matuƙi a filin jirgin saman Bagadaza ta kashe babban kwamandan Iran Qassim Soleimani.

An yi ta batun Iran za ta maida martani mai zafi kuma daga baya an ce ta yi hakan sai dai ba cikakkun bayanai na yadda ramuwar ta ƙasashe. Haƙiƙa mutuwar Soleimani ta konawa Iran rai matuka.

A nan an yi ta bayanin irin yaqe-yaƙen da Soleimani ya ƙulla da kare muradun soja na Iran a ƙasashen ƙetare. Dama shi aiki irin na Soleimani ka iya fuskantar irin wannan martanin ko a rayu ko a mutu.

Za mu fahimci Iran na daga ƙasashen duniya da ke da hannu a lamuran duniyar ko ma aƙalla ƙasashe da dama don kare muradun ta na addini, tattalin arziki da karfin faɗa a ji.

Shi ya sa ba mamaki Iran ke yunƙurin mallakar makaman ƙare dangi na nukiliya da duk wata babbar ƙasa ta ke mallakar su don zama garkuwa daga sauran abokan hamayya.

Sai mutum ya yi nazari da bincike mai tsawo ƙarfin fahimtar yadda ƙasashen duniya masu tasiri kan gudanar da lamuran su ko maida martani. Wasu lamuran sun wuce yadda a ke ganin su ko jin su a kafafen labaru.

Duniya kan dama da ƙasa mai dabara da hikimomin kauda-bara. Karfin kasa ma ya na dogara ga yawan ƙawayen da za su iya rufe ido su mara ma ta baya kan wani mataki ko ba ta da gaskiya.

Lamuran su na ƙara fitowa fili musamman in an samu kutsawar wata ƙasa ga lamuran wata kiasar. A kan yaqin Gaza ɗin nan an ga kasashe masu marawa Isra’ila baya na fitowa ƙarara su na yin hakan ko da a gefe guda a na ganin gawawwakin ƙananan yaran Falasdinawa iyayen su na kururuwar bakin cikin rabuwa da su a yanayi mai ban tausayi da takaici. 

Ita kuma Gaza sai ta fuskar tausayawa ba goyon bayan ƙasashe ba. A na dai saman ƙungiyoyin mayaƙa irin na houthi da hezbollah na mara mu su baya. Ko abinci a ka ce a shigar Gaza sai ya gagara don rashin uwa a murhu.

Iran ta ba da labarin harba makamai masu linzami kan Isra’ila.

Wannan na nuna ramuwar gaiya kan yadda Isra’ila musamman a kwanan nan ta kai hari kan cibiyar sojan Iran da ke daf da ofishin jakadancin ta a Damaskas inda hakan ya yi sanadiyyar rasa ran wasu jami’ai.

Ba a san irin illar da harin na Iran ya yi kan Isra’ila ba amma Iran ɗin ta ce harin ya kammala.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wanda ya ce mu su kule za su ce ma sa cas. Amurka da ke zama babbar kawar Isra’ila ta yi alwashin kasancewa da Iran a dukkan barazana daga Iran.

Zaman kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya kan harin da Iran ta ƙaddamar kan Isra’ila ya ƙare da nuna yatsa ta bambancin manufa tsakanin ƙasashe.

Harin na Iran ranar asabar ramuwar gayya ne ga harin da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancin Iran a Damaskas inda mutum 7 su ka rasa ran su.

Turkiya, Iraƙi da Jodan sun ce hakika Iran ta sanar da su don su kwana da sanin za ta kai harin.

Iran ta ce lalle ta sanar da Amurka batun harin kodayake Amurka ta musanta. Yanzu dai kamar an tsawata kan fitinar ta zarce haka duk da Isra’ila ta sha alwashin maida martani.

Majiyoyi sun nesanta Saudiyya daga shiga sahun waɗanda su ka tare hare-haren makamai masu linzami na Iran kan Isra’ila. Majiyoyin sun yi magana da kafar labaru ta Al-Arabiya da nuna Saudiyya ba ta hannu a tare makaman.

Wata kafa ta Isra’ila ce ta wallafa cewa Saudiyya ta shiga tare harin Iran na ranar asabar kan Isra’ila.

Iran dai ta cilla makamai da jirage marar sa matuƙa kan Isra’ila don ramuwar gaiya musamman kan harin Isra’ila kan ofishin jakadancin Iran a Damaskas.

Isra’ila ta ce ta kakkaɓo kashi 99% na makaman Iran duk da ba a tantance hakan daga majiya mai zaman kan ta ba.

Sarki Abdullah na Jodan ya ce qasar sa ba za ta zama cibiyar yakin Iran da Isra’ila ba.

Jodan dai na daga qasashen da su ka taimaki Isra’ila wajen kakkaɓo wasu daga makamai masu linzami da Iran ta harba.

Amurka, Burtaniya da Faransa ma na kan gaba wajen taya Isra’ila cabe makaman na Iran.

Da alamun Sarki Abdullah na kare matsayar Jodan ne kan rigimar ƙasashen biyu. Abdullah ya ce lalle Jodan za ta kare ‘yancin ƙasar ta ba tsaro kaɗai ba.

Tun farko ministan wajen Jodan Ayman Safadi ya zargi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da karkatar da hankalin duniya daga hare-hare kan Gaza zuwa dambarwa tsakanin ta da Iran.

Safadi ya ce tun da Iran ta ce ba ta son faɗaɗa yaqin daga ramuwar gaiya da ta yi to ba daidai ne Netanyahu ya yi ta yawo da batun harin ba.

A gaskiya siyasar duniya na shigowa sosai a wannan lamari da ya shafi Falasdinu da Isra’ila.

Ƙasashe musamman da ke hanyoyin da makaman Iran su ka ratsa na ambata masaniyar su kan lamarin bisa muradun a lamuran hulxar gwamnatocin su da manyan ƙasashen duniya masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya.

Kammalawa;
Ni dai ban ga yiwuwar fargabar wasu na cewa wannan takun saƙar ta Isra’ila da Iran za ta kai ga yakin duniya na uku ba. Kawai yanayin hare-hare musamman daga Isra’ila da sunan kare kai ko ɗauki ɗaɗɗaya ka iya faruwa.

Isra’ila na da manyan kasashen yammancin duniya a bayan ta inda Iran ke da na gabashi in hakan ya wakilci bayanan bisa ma’ana. Da alamu faɗan zai cigaba a ƙasashen da ke gewayen Isra’ila da Iran ke da sojojin ta da muradun ta a cikin su.

Abu mafi a’ala shi ne maida wuƙa kube. Hikimomi da dabarun bayan fage na Iran zai hana yammancin duniya ƙarfafa kai ma ta yaƙi don kasancewar ta Iran na taimakawa kai tsaye ko a kaikaice wajen raba gabar ta tsakiya gida biyu tsakanin ‘yan sunnah da ‘yan shi’ah. Duk da ba ranar tafiya tare sai dai hulɗar muradun MU RUFA WA KANMU ASIRI, amma samun azzama aƙidun sassan biyu na haifar da riba ta yadda manyan ‘yan sandan duniya za su cigaba da jan akalar duniya da fasahar shugabancin raba kan mabiya don samun sauƙin jagoranci wato logar “Divide and Rule” a Turance.