Da Ɗumi-ɗumi: Kano Pillars ta dakatar da kocinta Abdu Mai-Kaba

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Alh. Babangida Little, ya bayyana dakatar da mai horar da ‘yan wasan ƙungiyar, Abdu Maikaba, a ranar Talata.

Babangida Little ya bayyana dakatarwar da kuma kafa wani kwamiti wanda zai binciki kocin kuma idan aka same shi da laifi, to, zai fuskanci ladaftarwa.

Kawo yanzu ba a bayyana ainihin dalilin dakatarwar da aka yi masa ba, sai dai wasu na zargin furucin da Abdu Mai-kaba ya yi a lokacin wani taro da ƙungiyar magoya bayan Kano Pillars suka yi a cibiyar ‘yan Jaridu ta jiha ne ya haifar da dakatarwar.

A saurari ƙarin bayani….